Hotuna: Za a birne wani hamshaƙin attajiri tare da sunƙin daloli

Hotuna: Za a birne wani hamshaƙin attajiri tare da sunƙin daloli

- Masu kudin Zimbabwe sun dauki alkawarin ɗaukan naiyin bikin binne Ginimbi

- Iyalan Moana na neman kudin da zasu yi bikin jana'izarta daga masu fatan alheri

- Ginimbi da Moana sun rasu a hadarin mota ranar Lahadi yayin da suke dawowa daga wani taron shagali

Abokan wani attajirin Zimbabwe, Genius Kadungare wanda yafi shahara da Ginimbi a fagen zamantakewa sunce za a binne shi ne da tarin daloli, wata majiya ta kusa ta ruwaito.

Dan kasuwar wanda ya yi rayuwa ta alfarma, shine ya bar wasiyar, a cewar jaridar Herald.

Ginimbi ya rasu a wani hadarin mota daya afku ranar Lahadi a Harare tare da Mitchelle Amuli wadda aka fi sani da Moana.

Za a binne wani hamshaƙin attajirin Zimbabwe tare da daloli
Za a binne wani hamshaƙin attajirin Zimbabwe tare da daloli. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Iyalan Moana suna neman kudin jana'izarta daga masu fatan alheri kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Za a binne wani hamshaƙin attajirin Zimbabwe tare da sunƙin daloli
Za a binne wani hamshaƙin attajirin Zimbabwe tare da sunƙin daloli
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Wanda ya yi ƙarar Rahama Sadau ya ce fadar shugaban kasa da wani kwamishinan 'yan sanda ke hana a kama ta

Iyalanta sun dage jana'izarta zuwa sati biyu don jiran sakamakon gwajin kwayar halitta na DNA da kuma tattara kudaden da ake bukuta don yi mata suturar da ta dace, kamar yadda rahoton Zim Morning ya shaida.

Masu kudi a Zimbabwe sun ɗauki alkawari ɗaukan nayin bikin binne Ginimbi.

Wani mataimakin minista Tino Machakaire ya yi alkawarin siyawa Ginimbi akwatin gawa ƙirar Versace, dan majalisa Temba Mliswa ya bada tarin dabbobi don a yanka a wajen jana'izar, shi kuma wani dan siyasa, Acie Lumumba, ya yi alkawarin lita 1,000 na diesel, inji wata majiya ta kusa.

Za a binne wani hamshaƙin attajirin Zimbabwe tare da sunƙin daloli
Za a binne wani hamshaƙin attajirin Zimbabwe tare da sunƙin daloli
Asali: UGC

KU KARANTA: Rahama Sadau ta yi magana kan rahotannin kama ta da gurfanar da ita a kotu

Duka Ginimbi da Moana suna kan hanyarsu ta dawowa daga wani taron shagali ne motar su tayi karo da wata motar mai tahowa, kuma suka kauce daga titi tare da dukan wata bishiya kuma nan take ta kama da wuta.

A wani labarin, an samu rashin jituwa tsakanin mambobin kwamitin majalisar wakilai na tarayya kan 'yan gudun hijira a ranar Talata yayin zaman kare kasafin kudin Ma'aikatar JinKai da Kare Bala'i.

The Channels tv ta ruwaito wani dan majalisa, Fatuhu Muhammad ya fice daga zaman kwamitin majalisar yayin da ministan ma'aikatar Jin Kai, Sadiya Umar Farouk ke kare kasafin kudin ma'aikatar ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164