'Yan bindiga sun tafi har gidansa sun sace hakimi a jihar Zamfara

'Yan bindiga sun tafi har gidansa sun sace hakimi a jihar Zamfara

- Ƴan bindiga sun tafi gidan hakimin garin Matseri a Jihar Zamfara sun yi awon gaba shi

- Ƴan bindigan sun kuma sace yaran hakimin guda hudu a lokacin da suka tafi sace shi

- Har wa yau, sun kashe wani mazaunin garin da ya yi ƙoƙarin taka musu birki ya ceci hakimin

Wasu ƴan bindiga sun sace hakimin garin Matseri na da ke ƙaramar hukumar Anka a Zamfara, Alhaji Halilu Matseri da yaransa huɗu

Sun kuma kashe wani Maigaiya Matseri da ya yi ƙoƙarin ceto hakimin kamar yadda The Punch ta ruwaito.

'Yan bindiga sun tafi har gidansa sun sace hakimi a jihar Zamfara
Kwamishinan 'Yan sandan Zamfara, Usman Nagogo. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mijina ya yi min ƙaryar nice matarsa ta biyu, alhalin nice ta shida - Mata ta shaidawa kotu

Sarkin Anka wadda shine shugaban kwamitin sarakuna na jihar, Alhaji Attahiru Ahmed ya ce,"Ƴan bindigan sun afka garin a safiyar ranar Laraba inda suka yi awon gaba da hakimin da ƴaƴansa huɗu."

Wani mazaunin garin, Mallam Mohammed Musa ya ce ƴan bindigan sun taho garin a kan babura misalin kaɍfe 2 na dare.

KU KARANTA: Wanda ya yi ƙarar Rahama Sadau ya ce fadar shugaban kasa da wani kwamishinan 'yan sanda ke hana a kama ta

"Sun zo a kan babura sannan suka wuce gidan hakimin kai tsaye inda suka yi awon gaba da shi da yaransa guda huɗu.

Rundunar ƴan sandan Jihar ba tayi tsokaci kan lamarin ba a lokacin haɗa wannan rahoton.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, masu bincike a kasar Jamus a ranar Laraba sun ce sun fara bincike kan wasu da ake zargin sun sace fam miliyan 6.5 daga ofishin kwastam a ƙasar.

"An yi amfani da dabaru irin na ƙwararru yayin satar: uku cikin wadanda a yanzu ba a gano su ba sunyi amfani da na'urar huda abubuwa wurin shiga inda ake ajiye kuɗin," a cewar ƴan sanda.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel