Arewa: Akwai cin amana a tsakanin sojoji; rundunar soji ta koka

Arewa: Akwai cin amana a tsakanin sojoji; rundunar soji ta koka

- Rundunar soji ta ce kalubalen tsaro a yankin arewa na neman fin karfin gwamnatin Najeriya

- A cewar rundunar soji, hatta a tsakanin sojoji akwai cin amana

- A ranar Laraba ne sakataren gwamnatin kasar Amurka ya ce Amurka za ta taimakawa Najeriya ta fatattaki 'yan ta'adda

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa karfin soji kadai ba zai kawo karshen kalubalen tsaro da yankin arewa maso yamma da sauran sassan kasa ke fama da shi ba, tare da sanar da cewa "hatta a tsakanin sojoji akwai cin amana".

An fadi hakan ne yayin wani taro da rundunar soji ta yi da manema labarai daga Katsina da Zamfara wanda aka yi a sansanin soji na musamman da ke Faskari a jihar Katsina.

Rundunar sojin ta jaddada muhimmancin hada karfi da karfe a tsakanin hukumomin tsaro da sauran jama'ar farar hula domin samun zaman lafiya mai dorewa.

DUBA WANNAN: Sojojin Amurka sun kai hari kan 'yan bindigar arewacin Najeriya a kan Ba-Amurke guda daya

"Mun gaji da duk wannan zargi da jama'a ke yi wa rundunar soji a kan cewa su na kallo 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a yankin arewa maso yamma ba tare da yin komai a kan hakan ba," kamar yadda jami'in soji ya koka

Arewa: Akwai maciya amana a cikin sojoji; rundunar soji ta koka
Arewa: Akwai maciya amana a cikin sojoji; rundunar soji ta koka
Asali: UGC

"Hatta a cikin sojoji akwai maciya amana, shi yasa makiyanmu, 'yan bindiga, ke samun wasu muhimman bayanai"

Jami'in ya ce rundunar soji ba ta tare da 'yan bindiga kuma za ta cigaba da yakarsu.

DUBA WANNAN: Hukumomi 428 ba zasu iya biyan albashin watan Nuwamba ba; FG ta ankarar da ma'aikata

A cewar jami'in, jama'a su cigaba da taya rundunar soji da addu'a saboda batun tabarbarewar tsaro na neman ya fi karfin Najeriya.

Kazalika, ya bukaci jama'a su gaggauta bawa hukumomin tsaro goyon baya ta hanyar basu muhimmman bayanan da zasu kai ga kama 'yan bindiga tare da dawo da zaman lafiya a yankin arewa maso yamma.

Ya kara da cewa rundunar soji za ta adana sirrin duk wanda ya bata bayanai, a saboda haka kar jama'a su ji tsoro.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa sakataren gwamnatin ƙasar Amurka, Mike Pompeo, a ranar laraba, ya ce ƙasar Amurka zata yi amfani da dukkan makaman da take dasu don yaƙar ta'addanci a Najeriya da yammacin Afirika.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel