Buhari ya amince da gina sabbin cibiyoyin nazari da bincike 12 a Nigeria

Buhari ya amince da gina sabbin cibiyoyin nazari da bincike 12 a Nigeria

- Shugaba Buhari ya amince da gina wasu manyan cibiyoyin nazari da bincike guda 12 a fadin Najeriya

- TETFUND ce za ta dauki nauyin gina sabbin cibiyoyin a cewar Mallam Kashim Ibrahi Imam

- Imam ya ce shugaba Buhari na son ganin bincike da nazari ya zama jigon koyo da koyarwa a manyan makarantun Najeriya

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sahale a gina manya manyan cibiyoyin nazari da bincike guda 12 wadanda TETFUND za ta ɗauki nauyi daga kuɗaɗen shiga da hukumar FIRS ke tattarawa.

Shugaban amintattun TETFUND, Mallam Kashim Ibrahim Imam, ne ya bayyana hakan a lokacin taron zumunta tsakanin TETFUND da FIRS a ranar Talata a garin Port Harcourt.

Imam ya ce saboda son da Shugaba Buhari yake na ganin bincike da nazari ya zama jigon koyo da koyarwa a manyan makarantun gaba da Sakandire shine dalilin da yasa ya sahale a gina cibiyoyin binciken.

Ya ce haɗaka tsakanin TETFUND da FIRS ya tabbatar da ana samun kuɗin shiga ta hanyar tattaro haraji daga kamfanoni da mutane.

KARANTA: Muhimman hanyoyi 5 da mulkin Biden zai amfani Nigeria da nahiyar Afrika

Shugaban amintattun TETFUND yace da yawa daga cikin tsare-tsare da binciken da ake yi a makarantun gaba da sakandire na tarayya da jihohi TETFUND ce ke ɗaukar nauyi.

Buhari ya amince da gina sabbin cibiyoyin nazari da bincike 12 a Nigeria
Buhari @daily_trust
Asali: Twitter

Ya ƙalubalanci FIRS da ta maida hankali don tattaro biliyan ₦500 a shekarar 2020, kamar yadda ya tambayesu a baya da su tabbatar sun haɗa bilyan ₦277 a shekarar 2020 kafin karshen shekara.

KARANTA: Hukumomi 428 ba zasu iya biyan albashin watan Nuwamba ba; FG ta ankarar da ma'aikata

Imam yace,"tun bayan kafa TETFUND a shekarar 2011, kusan duk ayyukan manyan makarantu suka koma ƙarƙashinta"

Imam ya lissafo jadawalin ayyuka sama da guda 75 a jami'ar tarayyar ta Legas da wasu 68 a jami'ar jihar Legas da 68 a jami'ar Port Harcourt.

A wata hira da akayi da mai aiki a matsayin shugaban jami'ar ( V.C) Port Hacourt, Farfesa Stephen Okorodudu ya gasgata maganar Imam.

"Zan iya gasgata cewa anyi ayyuka 68 a jami'ata, wasu an kammala, wasu kuma ana kan yinsu, dukkansu ɗaukar nauyin TETFUND".

Taron zumuntar tsakanin TETFUND da FIRS mai taken "sabuwar hanyar buɗa tattara kuɗaɗen EDT lokacin annobar COVID-19 don gudanar da ayyukan da suka wajabta akan TETFUND".

Masu ruwa da tsaki da kuma manyan jami'an FIRS sun halarci taron.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa sanatoci sun bukaci gwamnatin tarayya ta yi koyi da takwararta Haɗaɗɗiyar daular Larabawa, UAE, wajen zaƙulo masu ɗaukar nauyin Boko Haram a Najeriya don ɗaukar matakin ladabtarwa da gaggawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel