Ni ne sabuwar ma'anar damokaradiyya, Obaseki yayin da yake daukar rantsuwa

Ni ne sabuwar ma'anar damokaradiyya, Obaseki yayin da yake daukar rantsuwa

- Gwamna Obaseki, ya ce yana kallon kansa a matsayin demokradiyya ita kanta

- A cewarsa kara zabensa a matsayin gwamnan Edo nasara ce daban

- Ya fadi hakan ne a lokacin da ake rantsar da shi a matsayin gwamna a karo na biyu

Godwin Obaseki, gwamnan jihar Edo ya kwatanta kansa a matsayin sabuwar ma'anar demokradiyya, The Cable ta wallafa.

Ya fadi hakan ne a ranar Alhamis, yayin da ake rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar a karo na biyu, wanda aka yi a Samuel Ogbemudia a Benin, babban birnin jihar Edo.

An yi taron rantsarwar gwamnan da ta mataimakinsa, Philip Shaibu.

A cewar Obaseki, lokaci ya yi da za a kawar da banbance-banbancen siyasa kuma a tabbatar ya ba kowa hakkinsa don taimakon mutanen jihar.

"Ina tsaye gabanku ne a bisa ikon Ubangiji da kuma jajircewar mutanen kirkin jihar Edo," a cewarsa.

"Zabena a karo na biyu alama ce ta nasara. Ina kallon kaina a matsayin ma'anar demokradiyya a Najeriya, kuma ina sane da duk wani nauyi da Ubangiji ya dora min," yace.

KU KARANTA: Budurwa ta bayyana barnar da tayi wa saurayinta bayan ta gano zai auri wata

Ni ne sabuwar ma'anar damokaradiyya, Obaseki yayin da yake daukar rantsuwa
Ni ne sabuwar ma'anar damokaradiyya, Obaseki yayin da yake daukar rantsuwa. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mutuwar Balarabe Musa babbar asara ce ga Najeriya da damokaradiyya, Ganduje yace

A wani labari na daban, an harbe wata alkalin kotu a kasar Philippines, a cikin harabar kotun da take alkalanci a birnin Manilla. Alkalin ta rasu bayan wani dan lokacin, sakamakon raunukan da ta samu saboda harbin.

Bayan 'yan sanda sun yi bincike, sun gano cewa akawun kotun, Amador Rebato, ne ya harbe alkalin mai suna Theresa Abadilla, daga bisani ya kashe kansa da kansa.

Har yanzu dai ba a samu wani bayani a kan dalilin da yasa akawun ya harbe alkalin ba. Sai dai kafafen yada labarai na kasar, sun ruwaito yadda aka yi ta kashe masu shari'a da dama, inda Abadilla ce mutum ta 51 da aka kashe tun bayan hawa mulkin shugaba Rodrigo Duterte a 2016.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel