Da ɗuminsa: Kotu ta garƙame wasu mata biyu da laifin yunƙurin kashe gwamna Oyetola

Da ɗuminsa: Kotu ta garƙame wasu mata biyu da laifin yunƙurin kashe gwamna Oyetola

- An gurfanar da wasu mutum biyu da ake zargi da kai wa Gwamna Oyetola hari a gaban kotu a jihar Osun

- Rundunar yan sandan ta fada ma kotu cewa wadanda ake zargin na daga cikin wadanda suka kai harin da ya yi sanadiyar lalata motoci 17 na gwamnan

- Sai dai kuma wadanda ake zargin sun nisanta kansu daga harin da aka kai kan Oyetola

Wata kotun majistare na Osun da ke zama a Oshogbo a ranar Laraba, ta garkame wasu mata biyu a gidan gyara hali na Ilesha kan zargin yunkurin kashe Gwamna Adegboyega Oyetola.

Matan da aka bayyana a matsayin Suliat Tajudeen mai shekaru 20 da Ayomide Abdulazeez mai shekaru 20, ana tuhumarsu da hada kai wajen yunkurin kisa, barna da kuma sata.

Dan sanda mai gabatar da kara, ASP John Idoko, ya sanar da kotu cewa Suliyat, Ayomide da wasu a ranar 17 ga watan Oktoban 2020, da misalin karfe 4:30 na rana, sun hada kai a yunkurin kashe Oyetola ta hanyar bude masa wutan harbi da jefarsa da duwatsu.

Ya kara da cewa sun lalata motoci 17 da ke a ayarin gwamnan.

KU KARANTA KUMA: An kai harin bam a wata maƙabarta a kasar Saudiyya

Da ɗuminsa: Kotu ta garƙame wasu mata biyu da laifin yunƙurin kashe gwamna Oyetola
Da ɗuminsa: Kotu ta garƙame wasu mata biyu da laifin yunƙurin kashe gwamna Oyetola Hoto: @StateofOsun
Asali: Facebook

Sun fasa shagon Justrite sannan suka sace na’urorin Laptop, wayoyin hannu da sauran kayayyaki da suka kai kimanin naira miliyan 3,568,000 mallakar Ashiru Ibrahim Olayemi.

Sai dai wadanda ake zargin basu amsa tuhume-tuhume biyar da yan sanda ke masu ba.

Lauyansu, Nurudeen Kareem, ya nemi a bayar da belin wadanda yake karewa inda ya ba kotun tabbacin samar da jingina abun dogaro.

Sai dai, mai kara ya nuna adawa da bukatar wanda ake kara, cewa idan aka basu beli za su gudu, saboda wadanda ake karar sun san cewa na da hujja a kansu.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Yan daba sun kai farmaki ofishin ƴan sanda, mutane 2 sun mutu

Alkalin kotun, Dr Ayilara ya tsare wadanda ake zargin a gidan gyara hali na Ilesha sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba 2020, don zartar da hukunci kan bukatar belin.

A wani labarin, an gurfanar da tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedioha Ohakim, a gaban wata babbar kotu a birnin tarayya kan zargin bayar da bayanan karya.

Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu ne ya gurfanar da Ohakim a kan wasu tuhume-tuhume uku a gaban kotun da ke Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng