Buhari ya amince da kashe N62.7bn domin gina titin Kano-Dawakin Tofa-Gwarzo-Dariyo

Buhari ya amince da kashe N62.7bn domin gina titin Kano-Dawakin Tofa-Gwarzo-Dariyo

- Shugaba Buhari ya jagorancin zaman majalisar zartaswa ranar Laraba

- Har yanzu, ministocin Buhari marasa kudirin gabatarwa na musharaka a ganawar ta yanar gizo

- An amince da muhimman ayyuka biyu a zaman yau

Majalisar zartaswan tarayya FEC karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta amince da amfani da kudi N62.7bn domin ginin titin Kano-Dawakin Tofa-Gwarzo-Dariyo a jihar Kano.

Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya sanar da hakan ranar Laraba yayin hira ga manema labarai, inda yake za'a kammala aikin cikin watanni 24 kacal, Daily Trust ta ruwaito.

Hakazalika, FEC ta amince da amfani da N470,263,037 wajen sayan kayayyakin horo a tashar jirgin saman Murtala Mohammed dake Legas.

KU KARANTA: Uwargidan shugaba Buhari, Aisha Buhari, ta bukaci a yi wa Najeriya addu'a

Buhari ya amince da kashe N62.7bn domin gina titin Kano-Dawakin Tofa-Gwarzo-Dariyo
Buhari ya amince da kashe N62.7bn domin gina titin Kano-Dawakin Tofa-Gwarzo-Dariyo Hoto: Presidency
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hukumomi 428 ba zasu iya biyan albashin watan Nuwamba ba; FG ta ankarar da ma'aikata

A bangare guda, jami'in binciken hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, Adariko Micheal, a ranar Laraba ya bayyana abinda akayi da kudin makaman da ake zargin Dasuki da karkatarwa.

Micheal ya ce an kashe N2.2 billion kan addu'ar kashe karshen Boko Haram a Najeriya da Sauidyya.

Jami'in ya bayyana hakan ne yayinda yake magana a matsayin shaida a kotu a shari'ar Sambo Dasuki, tsohon mai baiwa kasa shawara lokacin gwamnatin Jonathan wanda ake zargi da wawushe kudin makamai dala bilyan biyu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel