Uwargidan shugaba Buhari, Aisha Buhari, ta bukaci a yi wa Najeriya addu'a

Uwargidan shugaba Buhari, Aisha Buhari, ta bukaci a yi wa Najeriya addu'a

- Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta bukaci a sanya Najeriya a addu'a

- Aisha Buhari ta sanar da hakan ne a wata wallafa da ta yi a shafinta na kafar sada zumuntar zamani na Instagram

- Ta yi wallafar da kendir mai konewa inda ta kwararo wasu addu'o'i da harshen Larabci da kuma Turanci

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta bukaci a sanya kasar Najeriya a addu'a.

Aisha Buhari ta mika bukatar ne ta hanyar wallafar da tayi a shafinta na kafar sada zumuntar zamani na Instagram.

Ta yi wannan kiran ne a ranar Labara da safiyar 11 ga watan Nuwamban 2020.

Matar shugaban kasan ta yi wallafar a kan wata wutar kendir da ke konewa inda ta yi rubutu da harshen larabci da kuma Turanci.

Uwargidan shugaba Buhari, Aisha Buhari, ta bukaci a yi wa Najeriya addu'a
Uwargidan shugaba Buhari, Aisha Buhari, ta bukaci a yi wa Najeriya addu'a. Hoto daga punch.ng
Asali: UGC

Ta ce, "Allah ya isar mana kuma shine mafi alkhairin jagora. Shine mai bada kariya da kuma taimako."

KU KARANTA: Dakarun soji sun halaka 'yar kunan bakin wake tare da wasu mayakan ta'addanci

KU KARANTA: Batanci ga Annabi: Kungiya ta bukaci gwamnatin Kano ta kori ma'aikata 'yan Faransa

A wani labari na daban, shugaba Muhammadu Buhari ya ce matsawar yana kan mulki, 'yan Najeriya ba za su yi kukan rashin abinci ba.

Domin za a cigaba da noma don samar da abinda kowa zai kai bakin salatinsa. Shugaban kasar, ya fadi hakan a wani taro wanda NALDA ta shirya a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamba.

An shirya sabon tsarin don taimakon matasa a kan harkar noma. Shugaba Buhari ya ce zai yi iyakar kokarinsa wurin ganin ya bunkasa tattalin arzikin kasa wurin sayar da kayan gona ga kasashen ketare.

Shugaba Buhari ya ce yana so a dawo da noma a duk gonaki da aka dena noma acikinsu don bai wa matasa maza da mata damar yin noma.

A cewarsa, mulkinsa zai tabbatar an samu habaka a harkar noma, kuma hakan zai bayar da damar samun wadataccen abinci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel