Mun kashe N2.2bn wajen addu'ar kawo karshen Boko Haram - Abokin wawusan kudin makaman Dasuki

Mun kashe N2.2bn wajen addu'ar kawo karshen Boko Haram - Abokin wawusan kudin makaman Dasuki

- Wani shaida a shari'ar Dasuki ya bayyana makudan kudin da aka kashe wajen addu'a kadai

- Ya ce an yi amfani da ofishin Dasuki wajen tura kudade kamfanoni da asibiti

- Kotu ta wajabta sakin Sambo Dasuki bayan zargin almundahana 32 da gwamnati ke masa

Jami'in binciken hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, Adariko Micheal, a ranar Laraba ya bayyana abinda akayi da kudin makaman da ake zargin Dasuki da karkatarwa.

Micheal ya ce an kashe N2.2 billion kan addu'ar kawo karshen Boko Haram a Najeriya da Sauidyya, Premium Times ta ruwaito.

Jami'in ya bayyana hakan ne yayinda yake magana a matsayin shaida a kotu a shari'ar Sambo Dasuki, tsohon mai baiwa kasa shawara lokacin gwamnatin Jonathan wanda ake zargi da wawushe kudin makamai dala bilyan biyu.

Tare da Dasuki, ana zargin wani tsohon Manajan kamfanin NNPC, Aminu Baba-Kusa, kamfanin Acacia Holdings Limited, da asibitin Reliance Referral.

Mun kashe N2.2bn wajen addu'ar kawo karshen Boko Haram - Abokin wawusan kudin makaman Dasuki
Dasuki Hoto: Kotu
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Sabbin mutane 152 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 64,336

EFCC na zarginsu da laifuka 32 na almundahana, yaudara, rashin gaskiya da kuma amsan makudan kudi daga hannun wani Hussein Baba-Yusuf.

Yayin amsa tambayar lauyan EFCC, Rotimi Jacobs, Mr Micheal ya ce ofishin Dasuki ya tura kudi N750m asusun bankin asibitin Reliance Referral.

Ya kara da cewa an tura wani kudi N650m asusun bankin Acacia Holding Limited na Ecobank, yayinda aka tura N600m da N200m asusun bankin kamfanin na bankin UBA.

"Bisa sakonnin da muka samu daga bankunan, a matsayinmu na jami'an bincike, mun samu an tura makudan kudi asusun mutane da kamfanonin, " yace.

"Yayinda muka bibiyi kudaden, mun tambayi Aminu Baba-kusa dalilin haka."

"Ya ce an yi amfani da kudaden ne wajen daukan Malamai hayan addu'a don kawo karshen Boko Haram."

"Yayinda muka bukaci sunaye da lambobin Malaman da aka dauka, ya ambaci sunayen mutum biyu kadai."

Bayan sauraron maganar mai shaida, Baba-Yusuf ya dage zaman zuwa 11 ga Nuwamba domin cigaba da sauraron karar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel