Ba za a samu rashin abinci a karkashin mulkina ba, Buhari

Ba za a samu rashin abinci a karkashin mulkina ba, Buhari

- Shugaba Buhari ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa abinci ba zai tsinke musu ba

- A cewar shugaban, za a samu wadataccen abinci, don magance yunwa har a samu na siyarwa

- Ya ce Najeriya za ta cigaba da sayar da kayan abinci ga kasashen ketare don samun kudin shiga

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce matsawar yana kan mulki, 'yan Najeriya ba za su yi kukan rashin abinci ba. Domin za a cigaba da noma don samar da abinda kowa zai kai bakin salatinsa.

Shugaban kasar, ya fadi hakan a wani taro wanda NALDA ta shirya a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamba. An shirya sabon tsarin don taimakon matasa a kan harkar noma.

Shugaba Buhari ya ce zai yi iyakar kokarinsa wurin ganin ya bunkasa tattalin arzikin kasa wurin sayar da kayan gona ga kasashen ketare.

Shugaba Buhari ya ce yana so a dawo da noma a duk gonaki da aka dena noma acikinsu don bai wa matasa maza da mata damar yin noma.

A cewarsa, mulkinsa zai tabbatar an samu habaka a harkar noma, kuma hakan zai bayar da damar samun wadataccen abinci.

KU KARANTA: Da duminsa: Jigo a fadar Buhari ya rasu sakamakon ciwon kansa

Ba za a samu rashin abinci a karkashin mulkina ba, Buhari
Ba za a samu rashin abinci a karkashin mulkina ba, Buhari. Hoto daga @BashirAhmad
Asali: Twitter

KU KARANTA: Karen Biden, zababben shugaban Amurka zai kafa babban tarihi a duniya

Idan aka samu wadatar, har siyar da kayan abincin za ayi, don habaka tattalin arzikin kasa.

Yanzu haka na mayar da hankalina akan NADLA, don haka ina umartar ma'aikatar noma ta tarayya da ta jiha, da ta bayar da cikakken hadinkai ga NADLA.

Da bashin CBN, na tabbatar za a samu alheri a wannan shekarar.

A wani labari na daban, Gwamna Bala Mohammed ya nuna takaicinsa a kan yadda yakar Boko Haram yake daukar lokaci mai tsawo.

Gwamnan jihar Bauchin yayin da kwamitin 'yan majalisar wakilai a kan sojoji suka kai masa ziyara a gidan gwamnati a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba, ya ce wannan babban abin kunya ne a ce har yanzu ba a kawo karshensu ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel