Batanci ga Annabi: Kungiya ta bukaci gwamnatin Kano ta kori ma'aikata 'yan Faransa

Batanci ga Annabi: Kungiya ta bukaci gwamnatin Kano ta kori ma'aikata 'yan Faransa

- Malaman addinin jihar Kano sun bukaci Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi gaggawar dakatar da 'yan kasar Faransa daga yi wa jihar aiki

- Hakan ya biyo bayan sukar musulunci da shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron yayi, wanda hakan ya harzukar da musulman duniya

- Kungiyar ta isar da wannan sakon nata ne a wata takarda, wacce sakataren kungiyar, Dr Saidu Dukawa, ya saka hannu

Daukacin malaman addinin jihar Kano da ma'aikatu masu zaman kansu sun yi kira ga Ganduje a kan ya cire duk wani dan kasar Faransa daga yin ayyuka a jiharsa. Wannan ya biyo bayan sukar musulunci da Emmanuel Macron yayi, wanda hakan ya fusatar da musulman duniya.

Idan ba a manta ba, shugaban kasar Faransa, Macron, ya harzukar da musulman duniya, bayan ya bayyana niyyarsa ta yakar musulunci, sannan ya kwatanta imani da musulunci a matsayin lamarin da yake raba kawunan jama'a. Wannan al'amarin ya hassala musulman da ke fadin duniya.

Kungiyar Musulmai ta Kano, ta sanar da hakan a wata takarda da sakatarensu, Dr Saidu Dukawa, ya saka hannu.

Sun yi kira ga gwamnatin da tayi gaggawar musanya yaren Faransa da na Larabci a tsarin makarantun gwamnatin jihar.

Kungiyar ta hada da malamai masu karantar da litattafan addini da kuma na jami'a. Sun ce yin hakan ne kadai zai kawo kwanciyar hankali da zaman lafiya, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

KU KARANTA: Hotunan matashi mai shekaru 35 ya yi wuff da tsohuwa mai shekaru 80

Batanci ga Annabi: Kungiya ta bukaci gwamnatin Kano ta kori ma'aikata 'yan Faransa
Batanci ga Annabi: Kungiya ta bukaci gwamnatin Kano ta kori ma'aikata 'yan Faransa. Hoto daga @LindaIkeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Nagartattun halaye 9 na Bamalli da na duba na nada shi Sarkin Zazzau - El-Rufai

A wani labari na daban, Shugaban hukumar kananan hukumomi ta jihar Zamfara, Dakta Malami Aliyu Yandoto mai shekaru 57 a duniya ya yanke jiki ya fadi, tare da mutuwa a wurin bikin diyar Sanata Ahmed Sani Yerima da dan Sanata Adamu Aliero.

An yi daurin auren a gidan Yarima da ke Sokoto a ranar Asabar, 7 ga watan Nuwamban 2020 kuma ya samu halartar manyan 'yan siyasa, jiga-jigai da kuma kusoshin gwamnati da suka hada da shugaban majalisar dattawan Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel