Dakarun soji sun halaka 'yar kunan bakin wake tare da wasu mayakan ta'addanci
- Rundunar sojoji na cigaba da samun nasara a jihohin Borno da Yobe
- Sun samu nasarar kashe wata mata wacce ta je sansaninsu da abu mai fashewa
- Bacin sun ankare da wuri, da matar tayi musu kunar bakin wake, ta hallaka su
Rundunar sojoji ta kashe wata mata mai dauke da abu mai fashewa da wasu 'yan bindiga 7 a Borno da jihar Yobe, The Punch ta wallafa.
Matar, tayi yunkurin fasa abun a sansanin sojoji na 7 da ke Bama, jihar Borno, a ranar 3 ga watan Nuwamba, amma rundunar suka yi gaggawar kashe ta.
Kamar yadda takardar tazo a ranar Talata, daga mukaddashin darektan kakakin yada labarai, Birgediya janar Benerd Onyeuko, ya ce rundunar sojin ta sansani na 11 da aka mayar Gamboru, sun samu nasarar kashe 'yan Boko Haram 2 a maboyarsu da ke kauyen Bulama Lumbe da na Ndufu, wasu kuwa suka tsere da munanan raunuka.
"Sakamakon harin, rundunar ta kwato bindiga AK47 da tutocin Boko Haram guda 2," kamar yadda takardar tazo.
Sannan a ranar 7 da 8 ga watan Nuwamban 2020, rundunar ta 27 Task Force Brigade, wacce take a Buni Gari da ke karamar hukumar Gujba a jihar Yobe ta ragargaji wasu 'yan Boko Haram da suke yunkurin tayar da hankulan mutanen garin.
"Bayan wannan gumurzun, an kashe wasu 'yan Boko Haram 5."
KU KARANTA: Da duminsa: Jigo a fadar Buhari ya rasu sakamakon ciwon kansa
KU KARANTA: Nagartattun halaye 9 na Bamalli da na duba na nada shi Sarkin Zazzau - El-Rufai
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya ce ba zai bar tattaunawa da 'yan ta'addan jiharsa ba. Yace tattaunawar tana da matukar muhimmanci don neman zaman lafiya a jihar, Vanguard ta ruwaito.
Gwamnan ya sanar da hakan a wata takarda da Zailani Bappa, mai bashi shawara na musamman a harkar labarai, inda yace sun samu nasarar ceto mutane 26 daga jihar Katsina masu shekaru 8 zuwa 12 daga hannun 'yan ta'adda ba tare da biyan ko sisi ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng