Rundunar Soji ta fitar da sabbin sunayen 'yan ta'adda 81 da take nema ruwa a jallo

Rundunar Soji ta fitar da sabbin sunayen 'yan ta'adda 81 da take nema ruwa a jallo

- Rundunar sojoji ta ce nan ba da jimawa zata sake fitar da sunayen wasu yan ta'adda da take nema ruwa a jallo

- Gwamna Babagana Zulum ya shawarci yan ta'addan da su daina ayyukan ta'addancin su kuma rungumi zaman lafiya

- Akwai mashahuran irinsu Abu Dardda, Abu Maryam, Mallam Bako baya ga Abubakar Shekau da Abu Mus'ab Al-Barnawi

Rundunar sojojin Najeriya a ranar Laraba ta kaddamar da kashi na hudu na sunayen 'yan ta'addan Boko Haram wanda sunayen Abubakar Shekau da Abu Mus'ab Al-Barnawi ke kan gaba gaba da kuma wasu mutane 79 a cikin kunshin sunayen kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shekau, Abu Mus'ab da wasu 'yan ta'adda 79 da Rundunar Soji ke nema ruwa a jallo
Shekau, Abu Mus'ab da wasu 'yan ta'adda 79 da Rundunar Soji ke nema ruwa a jallo. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wanda ya yi ƙarar Rahama Sadau ya ce fadar shugaban kasa da wani kwamishinan 'yan sanda ke hana a kama ta

Kwamandan Lafiya Dole, Manjo Janar Farouk Yahaya ne ya bayanna haka a sansanin sojoji na Chabbal da ke Maiduguri yayin kaddamar da kashi na hudu na sunayen 'yan ta'addan.

"Munzo nan ne don kaddamar da kashi hudu na 'yan ta'addan Boko Haram, kamar yadda kuka sani, ba wannan ne karon farko ba, kuma zamu kaddamar da kashi na uku nan ba da dadewa ba," a jawabin Yahaya.

KU KARANTA: Rahama Sadau ta yi magana kan rahotannin kama ta da gurfanar da ita a kotu

A jawabinsa, gwamnan Borno, Prof. Babagana Zulum ya bukaci 'yan ta'addan da su daina barnar su kuma rungumi hanyar zaman lafiya.

Bayan kammala jawabin nasa, shugaban Sojin kasa na Najeriya Tukur Buratai ya mikawa Gwamna Zulum sunayen yan ta'addan

Daga cikin sunayen akwai Abubakar shekau, Abu Mus'ab Al-Barnawi, Modu Sulum, Umaru Tela, Iman Balge, Abu Umma, Mallam Bako (Hisbah), Abu Dardda, Ibrahim Abu Maryam daga cikin wasu da dama.

A wani labarin, an samu rashin jituwa tsakanin mambobin kwamitin majalisar wakilai na tarayya kan 'yan gudun hijira a ranar Talata yayin zaman kare kasafin kudin Ma'aikatar JinKai da Kare Bala'i.

The Channels tv ta ruwaito wani dan majalisa, Fatuhu Muhammad ya fice daga zaman kwamitin majalisar yayin da ministan ma'aikatar Jin Kai, Sadiya Umar Farouk ke kare kasafin kudin ma'aikatar ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel