Shugaba Buhari ya aika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan Balarabe Musa
- Shugaban kasa, Buhari, ya mika sakon ta'azziya ga daukacin al'ummar jihar Kaduna bisa rashin tsohon gwamna
- Balarabe Musa ya yi gwamnan Kaduna na tsawon shekara guda kafin aka tsigeshi
- Har karshen rayuwarsa ya kasance jagoran jam'iyyar Peoples Redemption Party PRP
Shugaba Muhammadu Buhari ya aika sakon ta'azziyarsa ga iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa, wanda ya rasu ranar Laraba, 11 ga Nuwamba, 2020.
Buhari ya siffanta Balarabe Musa a matsayin jajirtacce wanda yayi yaki tukuru wajen tabbatuwar demokridayya a Najeriya.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.
A cewarsa, Balarabe Musa "bai yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa an samu shugabancin kwarai a Najeriya."
KU KARANTA: Mun kashe N2.2bn wajen addu'ar kawo karshen Boko Haram - Abokin wawusan kudin makaman Dasuki
A bangare guda, daya daga cikin yaran marigayi Balarabe Musa, AbdulKasim Balarabe Musa, ya ce mahaifinsa ya rasu ne sakamakon bugun zuciya.
A hirar da yayi da jaridar Tribune, yace "tsawon wani lokaci yanzu mahaifi na na fama da matsala da zuciyarsa."
"Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ramalan Yero da wasu sun kai shi kasar waje domin jinyarsa amma tun daga lokacin, bai samu sauki ba, " yace.
"Mun ji dadi ya rasu da safen nan (Laraba) cikin baccinsa misalin karfe 8 na safe."
Bayan haka, shugaban jam'iyyar People’s Redemption Party (PRP), Alh Abdulrahaman Haruna, ya ce za'ayi jana'izarsa a Masallacin Sultan Bello misalin karfe 4 na la'asar.
KU DUBA: Firam Ministan Bahrain, Sheikh Khalifa bin Salman ya mutu
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng