Wani mutumi ya hallaka mutumin da yake zargi da neman matarsa bayan sakinta da kwana 3

Wani mutumi ya hallaka mutumin da yake zargi da neman matarsa bayan sakinta da kwana 3

- Bayan sakin matarsa da kwana uku, Umaru bai ji dadin ganinta da wani ba

- Yan sanda na neman shi ruwa a jallo da zargin laifin hallaka mutumin da ya gani tare da ita

- An ajiye gawan wanda ya kashe a dakin ajiye gawawwaki a Kaugama

Hukumar yan sandan jihar Jigawa, ta ce ana neman wani mutumi mai suna Umaru, wanda ake zargi da laifin kashe mutumin da yake zargi da neman tsohuwar matarsa.

Kakakin hukumar yansanda, SP Abdu Jinjiri, ya tabbatar da lamarin da ya auku ranar Litinin a Dakaiyawa, karamar hukumar Kaugama ta jihar, ga manema labarai ranar Laraba.

Jinjiri ya ce mutumin ya gudu bayan aikata aika-aikan kuma ana nemansa ruwa a jallo.

Kakakin yace Umar ya kashe mutumin ne don yana neman matarsa da suka rabu ba da dadewa ba.

"A ranar 9 ga Nuwamba, misalin karfe 3 na ranar, ofishin yan sanda dake kauyen Dakaiyawa a karamar hukumar Kaugama, ya samu rahoto cewa misalin karfe 2, Umar ya cakawa Sale Dange wuka."

"Wanda ake zargin ya caka masa wuka ne saboda ya ganshi da tsohuwar matarsa da ya saka bayan kwanaki uku kacal, "Mr Jinjiri yace.

Ya yi bayanin cewa ba tare da bata lokaci ba jami'an yan sanda suka garzaya wajen kuma suka kai gawar wanda aka kashe asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Kakakin ya kara da cewa tuni an ajiye gawarsa a dakin ajiye gawawwaki bayan bincike.

Ya ce an kaddamar da neman mutumin da yayi kisa, yayinda ake cigaba da gudanar da bincike.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya aika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan Balarabe Musa

Wani mutumi ya hallaka mutumin da yake zargi da neman matarsa bayan sakinta da kwana 3
Wani mutumi ya hallaka mutumin da yake zargi da neman matarsa bayan sakinta da kwana 3
Asali: Original

KU DUBA: Mun kashe N2.2bn wajen addu'ar kawo karshen Boko Haram - Abokin wawusan kudin makaman Dasuki

A wani labarin daban, wata budurwa ta farfasa gilasan tagar motar saurayinta saboda ta kama shi yana ha'intarta tare da wata.

Bidiyon wata budurwa ya yi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, wacce ke fasa gilasan jikin motar saurayinta.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, budurwar ta kama saurayinta dumu-dumu yana ha'intarta.

Mutane da dama sun yi ta cece-kuce a kan lamarin, inda suke cewa asarar dukiyar ta yi yawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel