Bidiyon budurwa tana ragargaza gilasan motar saurayi a kan cin amanarta da yayi

Bidiyon budurwa tana ragargaza gilasan motar saurayi a kan cin amanarta da yayi

- Bidiyon wata mata ya yi ta yawo a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram

- A bidiyon, an ga matar tana farfasa gilasan tagogin jikin mota cikin fushi

- An gano cewa motar saurayinta ne take fasa wa bayan ta gano yana ha'intarta

Wata budurwa ta farfasa gilasan tagar motar saurayinta saboda ta kama shi yana ha'intarta tare da wata.

Bidiyon wata budurwa ya yi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, wacce ke fasa gilasan jikin motar saurayinta.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, budurwar ta kama saurayinta dumu-dumu yana ha'intarta.

Mutane da dama sun yi ta cece-kuce a kan lamarin, inda suke cewa asarar dukiyar ta yi yawa.

Kamar yadda jaridar Legit.ng ta ga wani shafi na instagram mai suna Celebritiesbuzzgh, ya saka bidiyon, inda yayi tsokacin cewa lallai motar ta saurayin budurwar ne, kuma ta kama shi da wata budurwar ne, shine ta dauki wannan mummunan hukuncin a kansa.

Bidiyon budurwa tana ragargaza gilasan motar saurayi a kan cin amanarta da yayi
Bidiyon budurwa tana ragargaza gilasan motar saurayi a kan cin amanarta da yayi. Hoto daga celebritiesbuzzgh
Asali: UGC

KU KARANTA: Ku cigaba da tsananta addu'a a kan masu daukar nauyin Boko Haram, Zulum

Mutane da dama sun yi ta tsokaci iri-iri, wata ephyia cewa tayi: "Maimakon ki siyar da motar ba tare da ya sani ba, sai ki fasa mata taga."

Wani raddikalnonnies cewa yayi: "Idan ni ne, ba zan yi mata komai ba, zan ziyarci malami ne, don ya hada asusun bankinta da nawa... Kullum ta dinga turamin kudi ba tare da ta sani ba."

Wata mizk2805 tace: "Ina fatan matakin da kika dauka yasa kin huce."

KU KARANTA: Kotu ta bukaci a tsare dalibin da yayi wa mahaifiyarsa mugun duka

A wani labari na daban, bidiyon wata mata yayi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, wanda take bayyana yadda take rabuwa da kawayenta idan ta gano basu da saurayi ko miji.

Kuma ta shawarci duk wasu masu soyayya ko aure, da su rabu da kawayensu marasa masoya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng