Tsaka mai wuya: Kotu ta gurfanar da dan majalisar APC daga arewa saboda rantsuwa a kan karya

Tsaka mai wuya: Kotu ta gurfanar da dan majalisar APC daga arewa saboda rantsuwa a kan karya

- Kotun majistare da ke yankin Wuse, Zone 6, ta gurfanar da mamba majalisar wakilai daga mazabar Billiri/Balanga a jihar Gombe, Mista Victor Mela

- Rundunar 'yan sanda a birnin tarayya ta rubuta korafin zargin Mista Mela da rantsuwa a kan karya yayin da ya cike fom din INEC

- Lauyan da ke kare dan majalisar ya bukaci kotu ta yi sassauci a hukuncin da za ta zartar a kan Mista Mela

Wata kotun majistare da ke zamanta a Wuse, Zone 6, ta gurfanar da mamba a majalisar wakilai, Mista Victor Mela, bisa zarginsa da bayar da bayanan karya ga hukumar zabe ta kasa (INEC) tare da yin rantsuwa a kan cewa gaskiya ne.

Kotun ta ce dan majalisa Mela, mai wakilatar mazabar Billiri/Balanga a majalisar tarayya, ya bawa INEC bayanan karya domin samun damar tsayawa takara a zaben shekarar 2019.

Hukumar 'yan sandan birnin tarayya (FCT), Abuja, ce ta gurfanar da Mista Mela bayan zarginsa da rattaba hannu, a matsayin rantsuwa, a kan bayanana karya da ya bayar yayin cike fom din hukumar INEC mai lamba CF001 gabanin zaben 2019.

DUBA WANNAN: Ba haka bane Farfesa; Shehu Sani ya ci gyaran Zulum a kan sababin fara yakin Boko Haram

Alkalin kotun da ya saurari karar ya saka ranar yanke hukunci a kan karar bayan lauyan da ke kare Mista Mela ya nemi kotu ta yi sassauci a hukuncin da za ta zartar a kan wanda ya ke karewa.

Tsaka mai wuya: Kotu ta gurfanar da dan majalisar APC daga arewa saboda rantsuwa a kan karya
Victor Mela
Asali: Twitter

Hukumar INEC ta bayyana Mista Mela a matsayin wanda ya samu nasarar lashe zaben kujerar zaben dan majalisar wakilai na mazabar Billiri/Balanga a zaben da aka gudanar a cikin watan Fabarairu na shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta ware Dangote daga dokar rufe iyakokin kasa

Duk da Ali Isa, dan takarar jam'iyyar PDP, ya kalubalanci nasarar da Mista Mela ya samu a zaben, kotun turabunal da ta daukaka kara da ke Jos sun jaddada nasarar da dan takarar na APC ya samu.

A wani labarin daban da Legit.ng ta wallafa, an sake tsintar gawar matasan 'yammata biyu da mutanen da ba'a san ko su waye ba suka jefar a unguwar Kurmin Mashi da ke cikin garin Kaduna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel