Gwamnatin tarayya ta ware Dangote daga dokar rufe iyakokin kasa

Gwamnatin tarayya ta ware Dangote daga dokar rufe iyakokin kasa

- Gwamnatin tarayya ta yarje gami da sahalewa kamfanin siminti na Dangote ya cigaba da fitar da kayayyakinsa zuwa makwabtan ƙasashe duk da dokar rufe iyakokinta

- Tuni mutane suka fara sa ran cewa gwamnati za ta buɗe iyakar gabaɗaya don cigaba da gudanar harkokin kasuwanci tunda an fara buɗewa shafaffu da mai irinsu Ɗangote

- Tun a a watan Agusta na shekarar 2019 gwamnatin tarayya ta rufe iyakokinta don bunƙasa harkokin kasuwanci da noma a cikin gida

Gwamnatin Najeriya ta ƙyale kamfanin siminti na Dangote da yaci gaba da shige da ficensa akan iyakokin ƙasarta, a cewar jaridar Bloomberg.

Hakan ya zo duk da umarnin gwamnatin tarayya tayi na rufe iyakokin ƙasa sama da shekara guda.

Wannan yunƙuri ya janyo sa rai a zukatan ƴan Najeriya wai ko wataƙila gwamnatin tarayya na shirin buɗe iyakokin ƙasar don cigaba da kasuwanci da maƙwabtan ƙasashe bayan shafe sama da shekara guda a rufe.

Gwamnatin Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ta sahalewa babban mai sarrafa kaya na Afirka, Dangote, da ya cigaba da kai kayansa ƙasar Togo da Niger a watanni huɗun ƙarshen shekarar nan.

Wannan shine karo na farko a watanni goma, Michel Purchersos, shugaban kamfanin reshen jihar Legas, ya fada a wata hirarsa da masu ruwa da tsaki a kan hannun jari a Legas ya ce; "fitar da kayan ya kasance ne sakamakon sahalewar da gwamnati ta yi" a cewarsa.

KARANTA: Zamfara: Matawalle ya jagoranci kubutar da 'yammata 26 da 'yan bindiga suka sace a Katsina

Ana ganin ware kamfanin siminti na Dangote a matsayin laushi da gwamnatin ta yi akan matsayarta na rufe iyakoki da ya fara tun a watan Agusta na shekarar 2019.

Gwamnatin tarayya ta ware Dangote daga dokar rufe iyakokin kasa
Aliko Dangote
Asali: Facebook

Kamar kuma hakan zai baiwa kasuwanci cigaba da wanzuwa akan iyakokin ƙasar nan.

Gwamnatin Najeriya ta rufe iyakokinta da ƙashen da suka haɗar da; Benin da Nijar don kawo ƙarshen fasaƙwauri da bunƙasa harkokin kasuwanci cikin gida.

Dukda rufe iyakokin ya tilasta jama'a cin kayayyakin gona da aka sarrafa a gida Najeriya kamar shinkafa da sauransu.

KARANTA: A'a Farfesa; Shehu Sani ya ci gyaran Zulum a kan sababin fara yakin Boko Haram

Sai dai kuma hakan ya ƙuntatawa kamfanonin yammacin Afirka wanda suka dogara da Najeriya a kasuwancinsu na aƙalla mutane miliyan ɗari biyu ₦200m.

Dangote ya na fitar da kaya "amma a ƙayyade", sai dai akwai tsarin haɓaka kasuwancinsa ta hanyar amfani da mashigar teku acewar Puchercos.

Tsarin da kamfanin dake jihar Legas ke yi don ganin ta siyo hannayen jari ya samu jinkiri sakamakon tasgaro da tangarɗa irin ta kasuwa wanda hakan ya shafi darajar hannayen jarin,G uillaume Moye, mai aiki a matsayin babban shugaban kasuwanci shine ya faɗi hakan a wannan kiran tattaunawar haɗakar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng