Ba haka bane Farfesa; Shehu Sani ya ci gyaran Zulum a kan sababin fara yakin Boko Haram

Ba haka bane Farfesa; Shehu Sani ya ci gyaran Zulum a kan sababin fara yakin Boko Haram

- Gwamna Zulum ya ziyarci shugaba Buhari ranar Juma'a

- Bayan ganawarsu, Zulum ya gana da manema labarai tare da yin tsokaci a kan illar zanga-zanga saboda alakarta da Boko Haram

- Sai dai, tsohon Sanata Shehu Sani ya ce ba haka bane, ya bayyana tasa fahimtar

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya shawarci matasan Najeriya da su daina shiga zanga-zangar #EndSARS tare da yin kashedin cewa ƙungiyar Boko Haram, wadda ta addabi arewacin Najeriya, musamman arewa maso gabas, ta fara ne daga zanga-zanga.

Sai dai, tsohon sanatan tsakiyar jihar Kaduna, Kwamred Shehu Sani, ya ci gyaran Farfesa Zulum a kan wannan ikirari.

Farfesa Zulum ya bada shawarar ne jim kaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasa Muhammad Buhari a fadarsa dake Abuja.

A cewar Zulum, Boko Haram ta samo asali ne daga zanga-zanga akan dokar saka hular kwano.

Gwamnan yace,"Game da batun zanga-zangar #EndSARS, ina kira ga dukkan ƴan Najeriya musamman matasa da su kula sosai.

KARANTA: Babban dalilin da yasa aka tsige Rashidi Ladoja daga gwamna a shekarar 2006 - Obasanjo

"Dambarwar Boko Haram kacokan ta samo asali ne daga zanga-zangar da wasu matasa suka fara akan dokar saka hular kwano ga matuƙan babura. Kunga dai inda aka ƙare yanzu.

"Sama da mutane miliyan ɗaya sun rasa muhallinsu, kuma wanda abin yafi shafa sune matasa.

"Wasu daga cikin wanda suka jagoranci zanga-zangar sun bar jihar Borno, suna zaune a Abuja, Legas, ko ƙasashen waje.Ya kamata mu kula mu lura da kyau."

Ba haka bane Farfesa; Shehu Sani ya ci gyaran Zulum a kan sababin fara yakin Boko Haram
Ba haka bane Farfesa; Shehu Sani ya ci gyaran Zulum a kan sababin fara yakin Boko Haram
Asali: UGC

KARANTA: Obasanjo ya fadi abinda ya rusa takarar Atiku lokacin da yaso bijire masa a 2003

"Yanzu an fara samun zaman Lafiya a Jihar Borno, kuma bama son wani ya wargaza mana zaman lafiyar mu.

"Matasa suna tare damu, muna kula da su sosai, muna raba musu kayan abinci lokaci zuwa lokaci ko idan akwai buƙatar hakan.

"Muna basu tallafin kasuwanci,kuma a tunanina hanya mafi dacewa da kowanne ɗan Najeriya ya kamata ya nemi haƙƙinsa itace hanyar doka,idan ba haka ba babu inda zamu je.

Zaman lafiya nada matuƙar muhimmanci," a cewarsa.

Zaman lafiya dai yafi zama ɗan sarki.

Da yake mayar da martani a kan ikirarin Farfesa Zulum, tsohon sanata Shehu Sani ya ce kisa ba bisa ka'ida bane ya haddasa yakin Boko Haram, kamar yadda ya wallafa a shafinsa tuwita.

A daya bangaren, Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar babban bankin Najeriya (CBN) na rufe wasu asusun banki 19 mallakar wasu daidaikun mutane da kamfanonin da aka gano cewa suna da alaka da zanga-zanagar ENDSARS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel