Na yi imani cewa mace na iya gadar Buhari, In ji Amina Mohammed

Na yi imani cewa mace na iya gadar Buhari, In ji Amina Mohammed

- Tsohuwar ministar muhalli ta Najeriya, Amina Mohammed, ta kalubalanci mata da su zage damtse a 2023

- Amina ta ce ta yi imani mace na iya karbar mulki daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Ta bayyana hakan ne yayinda ta jagoranci tawagar manyan jami'an UN zuwa kasar domin tattauna mafita a kan barnar da annobar korona ta yi

Mataimakiyar babban sakataren majalisar dinkin duniya, Amina Mohammed, ta bukaci mata da su karbi mulki daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

Mohammed, wacce ta jagoranci wata tawagar manyan jami’an UN a ziyarar da suka kawo Najeriya, ta bayyana hakan ne yayinda take jawabi a wani shirin gidan talbijin a Abuja.

A ranar Litinin ne manyan jami’an UN sun gana da Shugaban kasar a Aso Villa a Abuja kan dabarun farfadowa bayan koma bayan da annobar COVID-19 ta haddasa.

Da take magana a ranar Talata, Mohammed ta ce ya zama dole dukkanin yan Najeriya su hada kai don sake gina kasar, ba tare da la’akari da banbancin kabila ko siyasa ba, jaridar Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Mahmood Yakubu: Shugaban INEC ya ce ci gaba da zama a kujerarsa zai zama ba daidai ba

Na yi imani cewa mace na iya gadar Buhari, In ji Amina Mohammed
Na yi imani cewa mace na iya gadar Buhari, In ji Amina Mohammed Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

“Akwai bukatar mu gane abunda yake ba daidai ba, mu yi aiki don ganin mun cimma nasara sannan mu san cewa za mu iya hakan ne a tare, kowannenmu na da hakki,” in ji ta.

Ta kara da cewa akwai bukatar mutunta kowani yanki na kasar nan “dukkaninmu muna da gudunmawar da za mu bayar."

Mohammed ta bayyana cewa Najeriya na iya samar da irin shugabanci da Afrika ke so ta hanyar aiki wajen cimma tsare-tsaren ci gaba mai dorewa na UN17 a 2030.

Da aka tambayeta ko za ta so mace ta gaji Buhari a matsayin Shugaban Najeriya, babbar jigon ta UN ta ce: “Wannan shine burina kuma ina ganin mace za ta iya. A koda yaushe mutum ya jajirce wajen neman wannan takara kuma kada ya gaza wajen gwada sa’arsa.

“Saboda haka, mata su tashi tsaye. Sune ke da kaso 50 na kuri’u sannan idan har za su iya nuna bajinta kamar namiji, mazan za su mara wa mata baya, toh mai zai hana? Babu wani dalili da zai hana mace iya jagorantar Najeriya.”

KU KARANTA KUMA: Za su iya daukaka kara: FG ta yi magana a kan ma su daukan nauyin Boko Haram (da aka yankewa hukunci a UAE)

Tsohuwar ministar muhallin ta Najeriya ta kara da cewa: “imma mace ko namiji abunda muke bukata shine dan Najeriya, mutum da ke kallon kasar nan a yadda take cikin hadin kai da karfinta da kuma tattauna hanyar kai ta ga mataki na gaba.

"Sai mun motsa daga magana da baki kawai zuwa aiwatarwa a aikace a dukkan kananan hukumomi 774, jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja. Wannan shine aikin da ake da bukatar yi kuma za a iya yi a karkashin shugabancin mace."

A wani labarin, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya yi gargadin cewa Najeriya na iya fuskantar sabuwar zanga zanga idan gwamnati ta gaza magance rashin aikin yi na matasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng