Babu abinda dakatad da Rahama Sadau zai canza a masana'antar Kannywood - Farida Jalal

Babu abinda dakatad da Rahama Sadau zai canza a masana'antar Kannywood - Farida Jalal

- Kamata yayi mu mayar da hankali kan cigaban Kannywood ba tsinewa juna ba, Farida Jalal

- Dakatad da Rahama Sadau ba zai canza kallon da ake yiwa yan Fim ba, cewar ta

Wata tsohuwar 'yar wasar kwaikwayo a masana'antar Kannywood, Farida Jalal, ta bayyana cewa dakatad da Rahama Sadau da kungiyar yan wasa MOPPAN tayi ba zai canza komai ba.

A hirar da tayi da jaridar Kano Focus, Farida Jalal ta ce hakan ba zai canza irin kallon da mutane suke yiwa 'yan wasan Kannywood ba.

Ta ce wannan ba shi bane karo na farko da za'a dakatad da Rahama ba amma har yanzu babu canjin da aka samu.

A cewar Faridar Jalal, ya kamata shugabannin kungiyar su samar da wata hanya na ladabtar da mambobinta da suke aikata laifuka irin na Rahama Sadau, ba kawai dakatad da su ko korarsu ba.

Ta kara da cewa mutane ba zasu daina yiwa Rahama Sadau kallon 'yar Kannywood ba, kuma duk abinda tayi wajibi ne a alakantashi da masana'antar.

"Wannan ba shi bane karo na farko da Rahama ke hakan ba kuma babu abun da ya canza. Saboda haka ban tunanin dakatarwa ko kora zai canza wani abu," ta ce.

"Abin damuwa shine dukkanmu a masana'antar muna Alla-wadai da tsine mata yayinda mu kanmu muna da kashi a gindi."

"Duk abinda ya faru da ita laifinta ne saboda tayi abinda bai dace ba. Amma tunda ta yi nadama kuma ta nemi hakuri, ya kamata mu yafe mata," ta kara.

Saboda haka ta yi kira ga abokan aikinta a masana'antar su hada kai kuma su mayar da hankali wajen cigaban masana'antar ba tsinewa juna ba.

Babu abinda dakatad da Rahama Sadau zai canza a masana'antar Kannywood - Farida Jalal
Farida Jalal Labari: Kano Focus
Asali: Facebook

KU KARANTA: Magidanci ya yi basaja a kafar sada zumunta, ya nemi lalata da matarsa, ta amince

A bangare guda, Reno Omokri ya yi amfani da shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda ya caccaki musulmai a kan zagin Rahama Sadau saboda rigarta mai bayyana tsirarici, amma suka yi shiru a kan satar da 'yan siyasa suke yi.

Reno ya wallafa hotunan musulmai mata da suke wasu kasashen, inda ya rubuta; "Yan Najeriya, wadannan hotunan mata musulmai ne daga kasar Egypt, Pakistan da Lebanon.

Kuna tunanin abinda Rahama Sadau ta aikata ya tsananta? Daga Musulunci har addinin Kirista bai halasta sata ba, amma muna alfahari da barayi.

KU KARANTA: Gara a rasa mulki amma a tsira da mutunci - Jonathan

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng