Mahmood Yakubu: Shugaban INEC ya ce ci gaba da zama a kujerarsa zai zama ba daidai ba

Mahmood Yakubu: Shugaban INEC ya ce ci gaba da zama a kujerarsa zai zama ba daidai ba

- Mahmood Yakubu ya ce ya sauka daga matsayin Shugaban INEC ne domin zai zama ba “daidai” ba idan ya ci gaba da zama a ofis

- Shugaban hukumar zaben ya kuma bayyana cewa yana jiran majalisar dattawa ta sake tabbatar da shi domin ya ci gaba da ayyukansa

- Shugaba Muhammadu Buhari ya sake nada Yakubu a karo na biyu, wanda hakan ya sa ya zamo Shugaban INEC na farko da zai dawo a zango na biyu

Daga karshe, Mahmood Yakubu, Shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), ya bayyana dalilinsa na mika mulki ga Muazu Ahmed duk da cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada shi a karo na biyu.

Da yake magana a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba, a hedkwatar INEC da ke Abuja, Shugaban hukumar zaben ya ce “zai zama ba daidai ba” ci gaba da aiki ba tare da majalisar dattawa ta tabbatar da shi ba.

Legit.ng ta tuna cewa Yakubu ya sauka na wucin gadi bayan ya mika shugabanci ga kwamishinan zabe Ahmed a ranar Litinin.

KU KARANTA KUMA: Za su iya daukaka kara: FG ta yi magana a kan ma su daukan nauyin Boko Haram (da aka yankewa hukunci a UAE)

Mahmood Yakubu: Shugaban INEC ya ce ci gaba da zama a kujerarsa zai zama ba daidai ba
Mahmood Yakubu: Shugaban INEC ya ce ci gaba da zama a kujerarsa zai zama ba daidai ba Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

Shugaba Buhari ya sake nada Yakubu a matsayin Shugaban INEC na wasu shekaru biyar masu zuwa a ranar Talata, 27 ga watan Oktoba.

Da yake mika jagorancin INEC ga Ahmed, Yakubu ya jaddada cewa ya zama dole a bi ka’idar kundin tsarin mulki tare da yi masa biyayya, kuma ma ya ajiye aikin ne na wucin gadi.

Ya bayyana cewa har zuwa lokacin da majalisar dattawa za ta tabbatar da shi, zai janye daga kasancewa Shugaban hukumar zaben Najeriya, Channels TV ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Korarre ne, tun a 2019 muka fatattaki Kabiru Marafa, in ji APC

A baya mun kawo cewa Farfesa Mahmoud Yakubu ya sauka daga kujerarsa a matsayin shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC).

Ya mika ragamar shugabanci ga kwamishinan zabe na kasa, Air Vice Marshal Muazu Ahmed mai ritaya, a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel