Minista Musulmi a Daular Larabawa ya goyi bayan kalaman shugaban Faransa

Minista Musulmi a Daular Larabawa ya goyi bayan kalaman shugaban Faransa

- Ministan ma’aikatar harkokin wajen daular Larabawa, Anwar Gargash ya goyi bayan Shugaban kasar Faransa kan cewa akwai bukatar addinin Musulunci ya tafi da tsarin al’ummar Yammacin Duniya

- Anwar ya ce Macron baya son ya mayar da al’ummar Musulmi saniyar ware a Yammacin Duniya ne kuma cewa maganarsa na kan hanya

- Ya kuma yi watsi da ikirarin cewa Shugaban Faransa na son mayar da al’ummar Musulmin da ke zaune a Faransa saniyar ware

Rahotanni sun kawo cewa wani ministan daular Larabawa, UAE, Anwar Gargash, ya bukaci al’umman Musulmi da su amince da matsayar Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron game da cewar akwai bukatar addinin Musulunci ya tafi da tsarin zamantakewa.

Gargash ya bayyana hakan ne yayin zantawa da jaridar Jamus a makon da ya gabata kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.

Matsayin ministan na zuwa ne a yayinda ake gudanar da zanga zanga a kasashen Musulmi domin Allah-wadai da kalaman Macron a kan addinin Musulunci, bayan ya zargi Musulmi da wariya.

KU KARANTA KUMA: IPOB na yunƙurin sake haddasa yaƙin basasa a Nigeria - Gwamnonin Kudu maso Gabas

Minista Musulmi a Daular Larabawa ya goyi bayan kalaman shugaban Faransa
Minista Musulmi a Daular Larabawa ya goyi bayan kalaman shugaban Faransa Hoto: @aminiyatrust
Asali: Twitter

Hakazalika Shugaban na Faransa ya kuma kare wani zanen batanci ga Annabi Muhammad (SAW) wanda ya haddasa cece kuce a duniyar Musulmi.

Ministan ya ce: “Ya kamata Musulmai su bude kunnuwansu da kyau su saurari abin da Macron ya fada a jawabinsa.

“Baya son ya mayar da al’ummar Musulmi saniyar ware a Yammacin Duniya, kuma maganarsa tana kan gaba.”

Ya ci gaba da cewa Musulmai na bukatar “su saje da tsarin da ya fi na yanzu” a kasashen Yammacin Duniya.

“Faransa na da hakkin zakulo hanyoyin da za a cimma hakan ta yadda za a yaki tsaurin ra’ayi da kuma gidadanci,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Neman mafita: An bankaɗo wani gwamnan PDP yana shirin komawa APC a wannan makon

Gargash ya yi watsi da zargin cewa Macron yana so ne ya mai da al’ummar Musulmin da ke zaune a Faransa saniyar ware.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng