Korarre ne, tun a 2019 muka fatattaki Kabiru Marafa, in ji APC

Korarre ne, tun a 2019 muka fatattaki Kabiru Marafa, in ji APC

- Babban jigon jam'iyyar APC a jihar Zamfara, Alhaji Lawal Liman ya ce sun dade da korar Sanata Kabir Marafa daga jam'iyyar

- Liman ya ce tun a shekarar 2019 suka dakatar da Marafa saboda yi wa jam'iyyar zagon kasa

- Ya yi zargin cewa Marafa baya nufin APC da alkhairi duba ga abubuwan da yake yi don haka jama'a su daina kallonsa a matsayin dan jam'iyyar

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Zamfara, Alhaji Lawal Liman, ya ce Sanata Kabiru Marafa ba dan jam’iyyar bane.

Liman ya ce: “Har yanzu Marafa korarre ne. Tun a shekarar 2019 jam’iyyar ta kore shi.”

Liman ya bayyana haka yayinda yake martani ga kalaman da aka alakanta da Marafa, inda yake zargin kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar ta kasa da rashin adalci, jaridar Punch ta ruwaito.

Korarre ne: Tun a 2019 muka fatattaki Kabiru Marafa, in ji APC
Korarre ne: Tun a 2019 muka fatattaki Kabiru Marafa, in ji APC Hoto: @GuardianNigeria
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Ahmed Musa, dan wasan Super Eagles, ya wallafa bidiyon sabuwar motarsa kirar Benz Vito

Ya ce: “A iya saninmu dai APC a Zamfara ta sallame shi, tun a 2019.

“Mun sallame shi daidai da kundin tsarin mulkin jam’iyyar sannan kuma mun gabatar da hukuncinmu zuwa ga hedkwatar APC ta kasa, Abuja.

"Don haka muna kira ga jama’a a kan kada su dauke shi a matsayin dan APC.

“Bama kallon Marafa a matsayin dan cikinmu saboda jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party na amfani da shi wajen haddasa manakisa a jam’iyyar.

“Kin biyayya ga hukuncin kwamitin uwar jam’iyyar ta kasa ya isa dalili na sanin cewa Marafa baya nufin APC da alkhairi.”

KU KARANTA KUMA: Neman mafita: An bankaɗo wani gwamnan PDP yana shirin komawa APC a wannan makon

A baya mun ji cewa Sanata Kabiru Marafa ya yi Alla-wadai da jinkirin Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wajen gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa.

Da yake magana a ranar Lahadi, Marafa ya koka a kan hukuncin kwamitin rikon kwarya na Gwamna Mai Mala Buni na Yobe da ya fara rijistan mambobi kafin taron.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel