Kwamishinan INEC, Abubakar Nahuche, ya sauka daga mukaminsa, wasu 5 sun yi ritaya

Kwamishinan INEC, Abubakar Nahuche, ya sauka daga mukaminsa, wasu 5 sun yi ritaya

- A ranar Litinin ne shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya mika mulki ga daya daga cikin kwamishinoninsa

- Farfesa Yakubu ya mika mulki ne bayan karewar wa'adinsa har zuwa lokacin da majalisar dattijai za ta sake tabbatar da shi a karo na biyu

- A farkon watan nan ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sake aika sunan Farfesa Yakubu zuwa majalisar domin ta sake tabbatar da shi a karo na biyu

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta tabbatar da cewa daya daga cikin kwamishinoninta, Abubakar Nahuche, ya ajiye mukaminsa.

Ya yi murabus ne 'yan mintuna kadan bayan shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya mika mulki ga Air Vice Marshall Ahmed Mu'azu, wanda zai jagoranci INEC kafin majalisar dattijai ta sake tabbatar da Farfesa Yakubu.

Festus Okoye, kwamishinan INEC mai kula da sashen ilimin masu zabe, ya tabbatar da murabus din Nahuche a cikin wani sako da ya wallafa ranar Litinin.

DUBA WANNAN: Buhari ya kafa kwamitin sayar da Kadarorin da aka kwato cikin wata 6

"Kwamishina a hukumar INEC kuma shugaban kwamitin ayyuka da sufuri wanda ya fito daga yankin arewa masi yamma, Abubakar Nahuche, ya ajiye mukaminsa saboda wasu dalilai na kasin kansa.

Kwamishinan INEC, Abubakar Nahuche, ya sauka daga mukaminsa, wasu 5 sun yi murabus
Farfesa Yakubu yayin mika mulki @inec
Asali: Twitter

"Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da murabus dinsa tare da yi masa godiyar hidimar da ya yi wa kasa," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Sunayensu: An yankewa ƴan Najeriya 6 hukunci a UAE bisa ɗaukar nauyin Boko Haram

Jaridar Punch ta rawaito cewa karin wasu kwamishinoni biyar a hukumar INEC sun yi murabus sakamakon cikar wa'adin aikinsu yayin da Farfesa Yakubu ya mika mulki a dakin taro na 'Rome' da ke hedikwatar INEC a Abuja.

Kwamishinonin sune kamar haka; Hajiya Amina Zakari, Farfesa Taiye Okoosi-Simbine, Alhaji Baba Shettima Arfo, Dakta Mohammed Mustafa Lecky, da Yarima Adedeji Solomon Soyebi.

Kazalika, yayin taron an nada Dakta Chukwuemeka Chukwu a matsayin sabon kwamishina a INEC da zai wakilci jihar Abia.

A ranar Litinin ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sanar da matasan da ke zanga-zangar ENDSARS a kan cewa ganin damarsu ce su rungumi zaman lafiya domin shi dai lokacinsa ya zo gangara, ya kusa tafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel