Buhari ya kafa kwamitin sayar da Kadarorin da aka kwato cikin wata 6

Buhari ya kafa kwamitin sayar da Kadarorin da aka kwato cikin wata 6

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa kwamitin sayar da kadarorin gwamnati da aka kwato daga hannun mabarnata

- Ministan shari'a, Abubakar Malami, ya rantsar da kwamitin ranar Litinin a Abuja

- Shugaban kwamitin, Dayo Apata, ya bayar da tabbacin cewa kwamitin zai yi aiki da gaskiya, ba tare da boye komai ba, wajen sauke nauyin da aka dora masa

Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin mutane 22 tare da bashi wa'adin wata shidda domin ya sayar da Kadarorin da aka kwato daga hannun mabarnata.

Ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ne ya sanar da hakan yayin rantsar da kwamitin a ranar Litinin.

A cewar Malami, tun a ranar 27 ga watan Oktoba, 2020, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da kunshin mambobin kwamitin.

Malami ya bayyana cewa; "an zakulo mambobin kwamitin ne daga hukumomin gwamnati ayyukansu da ke da alaka da yaki da cin hanci, rashawa, da ta'annati."

Ministan ya sanar da cewa Dayo Apata, babban mai nazarin shari'o'i a tarayya, shine zai jagoranci kwamitin.

KARANTA: Sunayensu: An yankewa ƴan Najeriya 6 hukunci a UAE bisa ɗaukar nauyin Boko Haram

A cewar Malami, daga cikin nauyin da aka dorawa kwamitin akwai gaggauta sayar da Kadarorin da aka kwato domin gwamnati ta samu kudaden shiga.

Buhari ya kafa kwamitin sayar da Kadarorin da aka kwato cikin wata 6
Abubakar Malami @TheCable
Asali: Twitter

"Aikinku shine tabbatar da sayar da dukkan kadarorin gwamnati da aka kwato tare da sayar da su a cikin Najeriya domin gwamnati ta samu kudin shiga cikin gaggawa.

"A saboda haka, ina son wannan kwamiti ya yi aiki da hukumomin gwamnati masu alaka da irin aikinsu domin samun saukin gudanar da aiki bisa tsarin doka.

KARANTA: A'a Farfesa; Shehu Sani ya ci gyaran Zulum a kan sababin fara yakin Boko Haram

"Ina fatan cewa wannan aiki da zaku yi zai zama sanadin samarwa gwamnati kudaden shiga da za a samu damar yi wa kasa aiki da su.

"Dole na gargadeku cewa ba karamin aiki bane a gabanku, akwai bukatar ku tsare kimar ku da ta kasarku. Akwai tsammani mai yawa a kanku," a cewar Malami.

A nasa jawabin, shugaban kwamitin, Apata, ya bayar da tabbacin cewa kwamitin zai yi aiki da gaskiya, ba tare da boye komai ba, wajen sauke nauyin da aka dora masa.

A ranar Lahadi ne Legit.ng ta rawaito cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Charles Agulanna, babban daraktan hukumar bunƙasa tsare-tsare (PRODA) bisa zarginsa da rashawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng