Buhari ya dakatar da babban daraktan hukumar nazari da bincike bisa zargin rashawa

Buhari ya dakatar da babban daraktan hukumar nazari da bincike bisa zargin rashawa

- Tun kafin ya hau mulki Buhari ya ke ikirarin cewa zai yaki cin hanci da rashawa

- A lokacin da ya ke yakin neman zabe, Buhari ya taba cewa; "idan Najeriya ba ta kashe cin hanci ba, cin hanci zai kashe Najeriya"

- Sai da, jama'a da dama sun zargi gwamnatin Buhari da yin amfani da hukumomi domin matsawa 'yan adawa da sunan yaki da cin hanci

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Charles Agulanna, babban daraktan hukumar bunƙasa tsare-tsare (PRODA) bisa zarginsa da rashawa.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shine ya fidda sanarwar a wata takarda da yasa hannu kuma ya aika ta zuwa ofishin ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu.

Takardar mai lamba SGF.6/S.19/T/211 na ɗauke da kwanan watan 5 ga watan Nuwamba.

DUBA WANNAN: Majiyar yan sanda ta bayyana dalilin gayyatar Rahama Sadau

A cewar takardar, an umarci Dani Onjeh, shugaban gudanarwa na hukumar da shima ya ajiye muƙaminsa.

Boss Mustapha ya ce darakta mafi girman matsayi da yake hukumar zai cigaba da jagorantar hukumar har sai ofishinsa ya kammala bincike.

Buhari ya dakatar da babban daraktan hukumar nazari da bincike bisa zargin rashawa
Dakta Agulanna
Asali: Twitter

"Na rubuta don cika umarnin bisa yarjewarsa kamar haka; "dakatar da Injiniya Dr C.N Agulanna babban daraktan hukumar bunƙasa tsare-tsare (PRODA) da ke Enugu, har zuwa lokacin da za'a kammala bincike", a cewar takardar.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kama shu'umin dan bindiga, Idi Dila 'Sarkin wayo', a Katsina

Sannan aka kara da cewa; "an gaggauta sauke Kwamared Daniel Onjeh, shugaban gudanarwa na hukumar PRODA har sai an kammala bincike"

Ana zargin Ogulanna da rarraba kwangila ba bisa ka'ida ba, barin aiki ba tare da izini ba, fitsara da rashin kunya, alfarma, aiki da kuɗi ta hanyar da basu dace ba, da kuma watsi da tsare-tsaren hukuma.

Sauran laifukan da ake zarginsa sun haɗar da ,wasarere da muhimman bayanai, aikata ɓarna, karɓar kuɗi ta hanyar barazana gami da tilasta ma'aikata da ƴan kwangila.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel