EndSARS: Sanata Adamu ya fallasa waɗanda su ke ɗaukar nauyin zanga zanga

EndSARS: Sanata Adamu ya fallasa waɗanda su ke ɗaukar nauyin zanga zanga

- Sanatan Najeriya, Abdullahi Adamu ya yi martani a kan zanga zangar EndSARS da ya gudana a wasu yankunan kasar a kwanan nan

- Adamu ya yi zargin cewa akwai makirci a zanga zangar

- Dan majalisar ya yi ikirarin cewa kudirin zanga zangar shine tunkudar da gwamnatin Buhari

Abdullahi Adamu, sanata mai wakiltan Nasarawa ta yamma, ya yi zargin cewa masu daukaka zanga zangar EndSARS na so su yi amfani da shi ne wajen sauya gwamnati.

Dan majalisar a yayin wata hira da jaridar Daily Trust, ya yi ikirarin cewa wasu manyan yan Najeriya ne ke daukar nauyin zanga zangar EndSARS domin kaskantar da arewa.

Adamu, wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Nasarawa tsakanin 1999 da 2007, ya ce idan da ace Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba dan arewa bane, da ba za a gudanar da zanga zangar ba.

EndSARS: Sanata Adamu ya fallasa waɗanda su ke ɗaukar nauyin zanga zanga
EndSARS: Sanata Adamu ya fallasa waɗanda su ke ɗaukar nauyin zanga zanga Hoto: Akelicious.net
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Ka gaggauta yin zaɓen shuwagabannin APC ko ka sauka daga riƙon ƙwarya - Marafa ga Buni

Dan majalisar ya ce:

“Mun ga wasu makirci a kan arewa a kasar Najeriya. Daya daga cikinmu shine Shugaban kasa a yau. Sannan ba za ku taba ganin irin wannan shirmen ba idan wanda ba dan arewa ba ya hau matsayin. Ina mai bayar da hakuri da danasanin fadin hakan, amma wannan shine zahirin gaskiya."

Adamu ya ce baya son ambatan sunayen mutanen da ke daukar nauyin zanga zangar amma dai zai ambata idan bukatar yin hakan ta taso.

KU KARANTA KUMA: Kariya zamu bata: Dalilin da ya sa rundunar ƴan sanda ta gayyaci Rahama Sadau

A gefe guda, wani rahoto daga jaridar The Nation ya nuna cewa akwai barazana na fara sabuwar zanga-zangar #EndSARS wanda bata gari suka kwace a baya.

A cewar rahoton, sabon ci gaban zai kasance ne sakamakon daskarar da asusun wasu shahararrun matasa da suka gudanar da zanga-zangar #EndSARS da aka yi.

An tattaro cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sami umurnin kotu don daskarar da asusun mutane da kungiyoyi 20 wadanda ke da nasaba da zanga-zangar ta #EndSARS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng