Da ɗuminsa: Babban kantin uwar gidan Ajimobi ya kama da wuta a Ibadan

Da ɗuminsa: Babban kantin uwar gidan Ajimobi ya kama da wuta a Ibadan

- Babban kantin uwar gidan Ajimobi ya kama da wuta a Ibadan

- A yanzu haka yan kwana-kwana na nan suna kokarin ganin sun kashe gobarar wacce ba a san musabbabinta ba

- Har ila yau an girke jami'an tsaro domin hana bata gari amfani da damar wajen yin sace-sace

Wani bangare na kantin Bodija da ke babban kantin Grandez mallakar uwar gidan tsohon gwamnan jihar Oyo, marigayi Abiola Ajimobi na nan yana ci da wuta.

Gobarar wacce ta fara daga bayan ofishin da ke kantin, na nan yana yaduwa a hankali zuwa aihanin manyan kantunan, jaridar The Nation ta ruwaito.

Jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Oyo, wadanda suka isa wajen a kan lokacci na nan suna gwagwarmayan hana wutar lakume dukkan kantin da kuma hana shi yaduwa zuwa gine-ginen da ke kusa.

Da ɗuminsa: Babban kantin uwar gidan Ajimobi ya kama da wuta a Ibadan
Da ɗuminsa: Babban kantin uwar gidan Ajimobi ya kama da wuta a Ibadan Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

An kuma gano jami’an tsaro na hadin gwiwa a wajen domin hana bata gari yin sata yayinda yan kwana-kwana ke kokarin kashe gobarar.

KU KARANTA KUMA: Kada ki bari ayi tonetone: Fati Slow ta yi kacakaca da Mansura Isa (bidiyo)

Bayan samun labari, Misis Ajimobi ta isa wajen tare da rakiyar wasu yan uwa da abokan arziki domin kula da halin da ake ciki.

Ba a san abunda ya haddasa gobarar ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Duk da kokarin da yan kwana-kwana ke yi, gobarar na ci gaba da ci a daidai wannan lokacin.

Sannan kuma an fara samun cunkoson ababen hawa a yankin.

KU KARANTA KUMA: Kariya zamu bata: Dalilin da ya sa rundunar ƴan sanda ta gayyaci Rahama Sadau

A wani labari na daban, mun ji a baya cewa ma’ajiyar tankokin mai na OVH da ke yankin Apapa a jihar Lagas na nan tana ci da wuta a yanzu haka.

Ba a san ainahin abunda ya haddasa gobarar ba wacce ta fara ci a safiyar yau Alhamis, 5 ga watan Nuwamba ba.

Sai dai kuma masu aikin ceto na ta kokarin kwashe mutanen da ke cikin harabar wajen a lokacin da gobarar ta fara, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng