Majiyar yan sanda ta bayyana dalilin gayyatar Rahama Sadau

Majiyar yan sanda ta bayyana dalilin gayyatar Rahama Sadau

- Har yanzu batun hotunan da jarumar Kannywood Rahamau ta wallafa na cigaba da haifar da cece-kuce a dandalin sada zumunta

- A ranar Asabar ne rahotanni suka bayyana cewa rundunar 'yan sanda ta gayyaci jaruma Rahama Sadau

- Kafin rundunar 'yan sanda ta gayyaci jarumar, wani Lauya ya shigar da kararta a gaban kotu a kan batun sakin hotunan

Wata majiyar yan sanda ta bayyanawa jaridar Daily Trust cewa rundunar bata yi niyyar kama Jarumar Kannywood Rahma Sadau ba, gayyatar da rundunar tayi mata tayi ne da nufin kareta da kuma kare afkuwar tashin hankali a jihar Kaduna.

Babban jami'in dan Sandan ya tabbatar da cewa Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu ya rubutawa Kwamishinan yan sandan jihar Kaduna, Umaru Muri, yana bashi umarnin ya binciki al'amarin da ya janyo batanci lokacin wata muhawara mai zafi akan dacewar hotunan da Rahama Sadau ta wallafa.

DUBA WANNAN: Ba haka bane Farfesa; Shehu Sani ya ci gyaran Zulum a kan sababin fara yakin Boko Haram

Yace sun bi Sadau Abuja inda ta koma da iyalanta saboda tsoron kada a cutar da ita kuma an girke jami'an yan sanda don dawo da ita Kaduna don amsa tambayoyi.

Majiyar yan sanda ta bayyana dalilin gayyatar Rahama Sadau
Rahama Sadau
Asali: Instagram

Wani da ya nemi a sakaya sunansa yace jami'an sun dawo Kaduna ranar Asabar ba tare da Sadau ba.

DUBA WANNAN: Babban dalilin da yasa aka tsige Rashidi Ladoja daga gwamna a shekarar 2006 - Obasanjo

"Ba wani umarnin kama ta, mun samu korafi da yawa akan ta kuma idan ka kalli wasikar Sufeto janar, ya umarci Kwamishina da ya tabbatar da zaman lafiya, kuma muna so muji daga gareta don muji irin barazanar da take fuskanta," a cewarsa.

Kafin rundunar 'yan sanda ta gayyaci jarumar, wani Lauya ya shigar da kararta a gaban kotu a kan batun sakin hotunan

Lauyan, ya gindaya sharudda 4 ga jarumar, wadanda yace wajibi ne ta cika su, tunda za a yi shari'ar ne a kotun musulunci.

Bayan gabatar wa da sifeta janar na 'yan sanda takardun korafi a kan kalaman batancinda aka yi wa manzon Allah (S A W) da hotunan Rahama Sadau suka janyo, kotu ta gindaya mata sharudda 4 da zata cika.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng