'Yan sanda sun kama shu'umin dan bindiga, Idi Dila 'Sarkin wayo', a Katsina

'Yan sanda sun kama shu'umin dan bindiga, Idi Dila 'Sarkin wayo', a Katsina

- Idi Dila 'sarkin wayo', matashin dan bindiga, ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Katsina

- Dila wata dabba ce mai matukar wayo da ke rayuwa a cikin manyan dazuka

- Saboda tsabar wayon dila, bata juya baya idan zata sha ruwa don gudun kar a kamata ko a kawo mata farmaki

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina, a ranar Alhamis, ta yi holin wani matashin dan bindiga mai shekaru 30 da ake kira da Idi Dila 'sarkin wayo'.

Dila wata dabba ce mai matukar wayo da tatsuniyoyi da labarai suka sha fadin cewa saboda tsabar wayonta, bata juya baya idan zata sha ruwa a gulbi ko korama, sai dai ta jika jelarta ta koma gefe ta tsotse ruwan.

Dabbar, wacce ke rayuwa a jeji, ta na yin hakan ne don kar a mamayeta a kamata ko kuma a kawo mata farmaki yayin da ta juya baya ta na shan ruwa.

Rundunar 'yan sanda ta yi zargin shu'umin dan bindigar na daga cikin 'yan bindigar da suka kai hari a kauyukan Diskuru da Kadsau inda suka kashe mutane fiye da goma sha biyu.

A cewar rundunar 'yan sanda, ta kama Dila, dan asalin kauyen Mumunu da ke yankin karamar hukumar Faskari, a ranar Lahadi.

KARANTA: Babban dalilin da yasa aka tsige Rashidi Ladoja daga gwamna a shekarar 2006 - Obasanjo

An gabatar da shi ga manema labarai tare da sauran wasu laifi 26 da ake zargi da aikata miyagun laifuka da suka hada da garkuwa da mutane da fashi da makami.

'Yan sanda sun kama shu'umin dan bindiga, Idi Dila 'Sarkin wayo', a Katsina
Wasu masu laifi da 'yan sanda suka kama a Katsina
Asali: Facebook

Yayin gabatar da masu laifin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah, ya ce sun kama Dila ne a Sheme a hanyarsa ta zuwa Faskari.

Isah ya ce Dila mamba ne a babbar kungiyar 'yan bindiga ta Melaya Alhaji Gandu wacce ta yi kaurin suna dajin Munhaye da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

KARANTA: Kotu ta bawa CBN izinin saka sakata a asusu 19 mallakar masu assasa zanga-zanga

Kazalika, rundunar 'yan sanda ta yi bajakolin daya daga cikin 'yan bindigar da ke tafka ta'asa a yankin dajin Rugu.

Dan ta'addar mai shekaru 26 ya shaidawa 'yan jarida cewa akwai hannunsa a wasu hare-hare da aka kai a kauyukan Ruma, Gwamra da Katoge.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce an gudanar da bincike a kan dukkan masu laifin kafin gurfanar dasu.

"Rundunar 'yan sandan jihar Katsin, a karkashin shugabancin kwamishin Sanusi Buba, ba zata bar masu laifi da 'yan ta'adda su sake ko rintsa ba," a cewarsa.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa Rundunar sojin saman Nigeria (NAF) ta ce zata tura da jiragen sama marasa matuki zuwa jihar Zamfara don bunkasa aikinta na yaki da 'yan bindiga a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel