A raba ni da shi, gagarumin mashayi ne kuma yana dukana - Matar aure ga kotu

A raba ni da shi, gagarumin mashayi ne kuma yana dukana - Matar aure ga kotu

- Wata Munirat Obaro, ta roki kotu ta raba aurensu da mijinta Abdullaziz Mohammed

- Ta ce mijin nata yana shaye-shaye, yana kuma dukanta har da yunkurin kasheta

- Alkalin ya ce bata kawo gamsassun hujjoji ba, don haka yaki raba auren

Wata matar aure mai suna Munirat Obaro, ta roki wata kotu da ke zama a Gwagwalada ta raba aurenta na shekara 17 da mijinta, Abdullaziz Mohammed, wanda ta ke zarginsa da shaye-shaye.

Munirat, mai yara 4, wacce take zaune a Anguwar Shani, ta zargi mijinta da dukanta akai-akai har da yunkurin kasheta.

Mohammed ya musanta zargin da take yi masa, inda yace "Matata tayi min kazafi, duk da a shirye nake da na canja duk halayena wadanda bata so."

KU KARANTA: CNG ta caccaki gwamnonin arewa, ta ce sun nuna rashin muhimmanci ga tsaro, matasa da talauci

Alkali mai shari'ar, Adamu Isah, ya ce shaidun da ta gabatar a gaban kotu basu da karfi don haka kotu ta ki amincewa da raba auren.

Yace su cigaba da zama a matsayin mata da miji, Daily Trust ta wallafa.

A raba ni da shi, gagarumin mashayi ne kuma yana dukana - Matar aure ga kotu
A raba ni da shi, gagarumin mashayi ne kuma yana dukana - Matar aure ga kotu. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: IGP ga 'yan sanda: Ku gaggauta komawa wuraren aikinku

A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya ya wallafa hirarsa da budurwar a kafafen sada zumuntar zamani. Ya wallafa yadda suka yi da ita bayan ta cire kudi daga asusun bankinsa ba tare da izininsa ba.

Kamar yadda hirar ta nuna, budurwar ta nuna rashin nadamarta a kan abinda tayi, sai dai kuma ta bi hakan da korafin cewa baya kula da ita yadda ya dace.

Matashin da ya kasa boye fushinsa ya ja kunnenta a kan sake taba masa kudin asusun bankinsa ba tare da izininsa ba amma ta ce ba za ta daina ba.

Ta tabbatar masa da cewa wasu mazan na nan a kan layi kuma idan ba ya kulawa da ita, za ta karkata garesu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel