Dubunnan mutane sun yi zanga-zanga kan batancin da aka yiwa manzon Allah (SAW) a Senegal

Dubunnan mutane sun yi zanga-zanga kan batancin da aka yiwa manzon Allah (SAW) a Senegal

- Ba'a bar kasar Senegal a baya ba, sun nuna bacin ransu kan zanen batanci ga Annabi Muhammadu (SAW)

- Daya daga cikin masu zanga-zangan ya ce shi yanzu ya ki jinin shugaban kasar Faransa, Macron

Dubunnan mutane sun yi zanga-zanga a babbar birnin Senegal, Dakar, ranar Asabar kan zanen batancin da akayi wa manzon Allah (SAW) da kuma kare hakan da shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ke yi.

Yan jaridan AFP sun ruwaito masu zanga-zangan suna kona tutocin kasar Faransa da hotunan shugaban kasan kuma suna kira ga kauracewa kayayyakin kasar Faransa a kasashen Musulmai.

"Macron ya jiwa Musulman duniya rauni. Idan duniya ta zauna lafiya, aikin addinin Islama ne. Na ki jinin Macron," wani mai zanga-zanga Youssoupha Sow, yace.

Zanga-zanga ya barke a kasashen duniya bayan kalaman shugaban kasar Faransa, inda ya lashi takobin fito-na-fito da Musulunci da kuma kare masu zanen batanci ga manzon Allah saboda kowa na da yancin abinda ya ga dama.

Kashi 95% na kasar Senegal Musulmai ne kuma Faransa ta basu yancin kai.

Daya daga cikin masu zanga-zangan Marcer Awa Thiam yace: "Ba wai muna yaki Faransa bane. kawai muna son yan'uwanmu Musulmai su yi addininsu cikin kwanciyan hankali."

"Bai kamata ana ba mutane tsoro ba, cewa addinin Musulunci addinin ta'addanci ne ko mugunta... maganar gaskiya itace babu addini mafi zaman lafiya kaman Musulunci."

Wani mai zanga-zangan, Kara Sow yace "Muna son Manzon Allah fiye da iyayenmu."

KU KARANTA: Hukumar yan sanda ta sammaci Rahama Sadau, bayan hotunanta sun haddasa kalaman batanci

Dubunnan mutane sun yi zanga-zanga kan batancin da aka yiwa manzon Allah (SAW) a Senegal
Dubunnan mutane sun yi zanga-zanga kan batancin da aka yiwa manzon Allah (SAW) a Senegal Credit: Seyllou / AFP
Asali: UGC

A wani labarin daban, Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya ce kasarsa na yaki da tsatsaurin ra'ayin Musulunci ne, amma ba da addinin Islama ba.

Macron ya bayyana hakan ne yayinda yake martani kan labarin da kamfanin jaridar Financial Times ya wallafa inda yace an yi masa mumunan fahimta kuma daga baya an cire labarin da shafin yanar gizon jaridar.

KU KARANTA: IGP ya janye yan sandan dake kare Fani Kayode, Sanatoci, manyan malamai da masu kudi a fadin tarayya

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel