Da duminsa: El-Rufai ya yi magana a kan fastocinsa na takarar shugabancin kasa

Da duminsa: El-Rufai ya yi magana a kan fastocinsa na takarar shugabancin kasa

- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya musanta sanin wanda ya ke da alhakin hada hotunansa a fostoci a matsayin dan takara

- A cewar gwamnan, ba shi da niyyar neman takarar mataimakin shugaban kasa a 2023, amma daga nan bai san abinda gobe za ta haifar ba

- Gwamnan ya fadi hakan a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a Abuja, inda yace yanzu haka yana so ya zama gwarzon gwamna

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya musanta sanin masu hada hotunansa a fosta da sunan kamfen dinsa a matsayin mataimakin shugaban kasa a zaben 2023 dake gabatowa.

Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan haduwarsa da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a fadar shugaban kasa da ke Abuja, ranar Juma'a.

Gwamnan jihar Kaduna ya ce har Amaechi ya kira amma ya ce shi sam bai san wadanda suka yi ta hada hotunansu a takardu suna mannawa ba, Vanguard ta wallafa.

A cewarsa, "Ina da burin zama gwamnan da yafi kowanne nagarta da aiki, kuma ina yin iyakar kokarina wurin ganin nayi wa jihata ayyuka yadda yakamata, daga yanzu har 2023. Amma bayan 2023, zan bar komai a hannun Allah.

Gwamnan ya kara da bayyana yadda matsalar rashin tsaro da ke jiharsa take ci masa tuwo a kwarya. Da yadda masu garkuwa da mutane suka kara yawa, yana da burin ganin ya magance wadannan matsalolin tukunna.

KU KARANTA: EndSARS: IGP ya zargi kafafen sada zumunta da assasa rikici

Da duminsa: El-Rufai ya yi magana a kan fastocinsa na takarar shugabancin kasa
Da duminsa: El-Rufai ya yi magana a kan fastocinsa na takarar shugabancin kasa. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: UGC

KU KARANTA: Tsaro: Matawalle ya saka wa sarakunan gargajiya da wasu shugabanni sabon takunkumi

A wani labari na daban, Sufeta janar na 'yan sanda Adamu Mohammed, ya shawarci 'yan sanda da su yi amfani da makamansu a duk lokacin da su ka fuskanci wani hatsari, jaridar The Nation ta wallafa.

Sufetan ya bayar da wannan shawara ne a 'yan kwanakin nan yayin da ya ke yin jawabi ga jami'an 'yan sanda. A halin yanzun, Adamu ya na tafiye-tafiye zuwa jihohi daban-daban domin duba irin barnar da bata-gari su ka yi ga hukumar ta 'yan sanda a lokacin zanga-zanga ta EndSARS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel