Kotu ta bawa CBN izinin saka sakata a asusun masu assasa zanga-zanga a Nigeria

Kotu ta bawa CBN izinin saka sakata a asusun masu assasa zanga-zanga a Nigeria

- Tun a cikin watan Oktoba babban bankin kasa ya nemi izinin kotu domin rufe wasu asusun banki 19

- CBN ya nemi izinin rufe asusun ne bisa zargin cewa ana amfani da su wajen rura wutar zanga-zangar ENDSARS

- Zangar-zangar lumana ta ENDSARS da aka fara a wasu biranen Najeriya ta rikide zuwa kazamin rikici

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar babban bankin Najeriya (CBN) na rufe wasu asusun banki 19 mallakar wasu daidaikun mutane da kamfanonin da aka gano cewa suna da alaka da zanga-zanagar ENDSARS.

Tun a ranar 20 ga watan Oktoba CBN ta nufi kotun domin neman ta bata izinin rufe asusun 19, amma sai ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamba, kotu ta amince da bukatar, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Wasu daga jagorin zanga-zangar ENDSARS sun yi korafin cewa an hanasu barin Najeriya a yayin da suka yi niyyar ficewa daga kasar.

KARANTA: Babban dalilin da yasa aka tsige Rashidi Ladoja daga gwamna a shekarar 2006 - Obasanjo

CBN ta nemi rufe asusun ne bisa zargin cewa wasu mutane da kamfanoni suna amfani da kudi domin rura wutar zanga-zangar ENDSARS.

Jaridu sun kawo labaran yadda aka dinga walima da rabon kayan kwalam da makulashe a wuraren taron gangamin da masu zanga-zangar ENDSARS suka yi a wasu biranen Najeriya.

Kotu ta bawa CBN izinin saka sakata a asusun masu assasa zanga-zanga a Nigeria
Kotu ta bawa CBN izinin saka sakata a asusun masu assasa zanga-zanga a Nigeria
Asali: Twitter

Gwamnati ta yi zargin cewa wasu mutane da kungiyoyi sun saka hannun jari a zanga-zangar domin yamutsa kasa da kuma cimma boyayyun manufofinsu.

KARANTA: Zamfara: Rundunar soji ta baza jiragen yaki na zamani masu leken asiri da ruwan wuta

Zanga-zanagar ENDSARS, wacce aka fara a matsayin ta lumana, ta rikide zuwa rikici a jihohin da ta samu karbuwa.

Sai dai, rikicin da ya barke sakamakon zanga-zangar ya shafi hatta jihohin da zanga-zangar bata yi wani armashi ba.

A yayin da gwamnati ke zargin masu zanga-zangar ENDSARS da zama silar barkewar rikicin, masu zanga-zangar na zargin gwamnati da dauko hayar 'yan ta'adda domin batawa zanga-zangar ENDSARS suna.

Daya daga cikin jagororin zanga-zangar, 'yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu, ta yi shagube yayin da take martani ga Musulman da suka dinga caccakarta saboda 'ta yi uwa, ta yi makarbiya' yayin zanga-zangar ENDSARS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel