Wilbur: Hotunan karen da ya lashe zaɓen kujerar magajin gari a Amurka
- Kare mai suna Wilbur ya lashe zaben kujerar magajin gari a wani yanki na jihar Kentucky mai suna Rabbit Hash a Amurka
- Tun shekaru da dama dabobi ne ake zaba a matsayin magajin gari a Rabbit Hash kuma har yanzu
- Kawo yanzu karnuka biyar ne suka rike mukamin magajin garin a tarihin garin na Rabbit Hash
Wani kare mai suna Wilbur mai watanni shida da haihuwa ya lashe zaben kujerar magajin gari (mayor) a Amurka. An zabe shi a matsayin magajin garin Rabbit Hash da ke Jihar Kentucky.
A cewar mai magana da yawun Wilbur - wadda shine mai karen, Amy Noland - wannan karamin garin da ke da al'umma kasa da 500 bai taba zaben dan adam a matsayin magajin gari ba.
DUBA WANNAN: Mutanen gari sun fatattaki 'yan bindigan da suka kai musu hari a Zamfara
Wani mutumin garin a shekarun 1990s ne ya bada shawarar zaben dabobi a matsayin 'magajin gari' yayin wani taron neman tallafi na kungiyar tarihi kamar yadda Noland ya shaidawa NBC News.
Wilbur ya yi nasara kan Brynneth Paltrow da ke kan mulkin a yanzu kamar yadda LIB ta ruwaito.
A cewar wata mujallar Louisville, Wilbur ya samu kuri'u 22,985 wadda shine mafi yawa da aka taba kada wa a zaben garin.
Kawo yanzu karnuka biyar ne suka rike mukamin na 'magajin gari' a Rabbit Hash tun magajin garin na farko mai suna Goofy.
KU KARANTA: Ba ku isa kuyi mana mulkin mallaka ba - Kungiyar Dattijan kudu ga gwamnonin Arewa
Kawo yanzu, Noland ya ce Wilbur ya fara daukan sabon aikinsa da muhimmanci inda ya ke yawo a gari ana 'shafar cikinsu da kunensa'.
A wani labarin, magoya bayan shugaban Amurka, Donald Trump, cikinsu ana zargin wasu na ɗauke da bindigu, sun zagaye ofishin zaɓe na Maricopa County da ke Arizona suna zanga-zanga kan zabe.
Wani bidiyo da aka nuna a CNN, ya nuna magoya bayan Trump ɗauke da saƙonni da ke nuna rashin jin daɗinsu kan hasashen da ke nuna jam'iyyar Democrats za ta yi nasarar cin kwallejin zaɓe 11 a jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng