Bayan nadamar ta: Rahama Sadau ta bayyana halin da take ciki na rashin kwanciyar hankali

Bayan nadamar ta: Rahama Sadau ta bayyana halin da take ciki na rashin kwanciyar hankali

- Jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta bayyana halin da take ciki na rashin kwanciyar hankali bayan nadamar da tayi

- Rahama ta ce ta zama abun tausayi a yanzu sakamakon batancin da aka yi wa Annabi a karkashin hotonta

- Ta kuma ce ta ji zafi a kan yadda jaruman Kannywood suka dunga maganganu kan lamarin maimakon su ankarar da ita

Shahararriyar jarumar Kannywood, Rahata Sadau, ta bayyana cewa ta zama abin tausayi sakamakon hotunanta da ta saka wadanda suka haddasa cin mutunci ga addininta.

Rahama wacce tun da fari ta fito ta nuna nadama a kan wallafa hotunan da ta yi, bayyana cewa ta ji zafi matuka kan yadda abokan sana’anta suke ta maganganu kan al’amarin. Ta jaddada cewa abun ya faru ne ba tare da san ranta ba.

A hirarta da sashin BBC, Rahama ta ce duk wani mai hankali idan ya nutsu ya dubi abin da ya faru zai gane cewa ta zama abin tausayi.

"Wani ya kamata ya yi tunanin shin ya Rahama take ji a matsayinta na musalma," in ji ta.

KU KARANTA KUMA: Rahama Sadau ta nemi afuwa bisa sabbin hotuna da ta fitar

Bayan nadamar ta: Rahama Sadau ta bayyana halin da take ciki na rashin kwanciyar hankali
Bayan nadamar ta: Rahama Sadau ta bayyana halin da take ciki na rashin kwanciyar hankali Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

Ta ce da dare ta saka hotunan ta tafi ta yi bacci, ba tare da ta tsaya bibiyar me ake cewa ba game da hotunan da ta wallafa.

"Sai da gari ya waye ina tashi na ga sharhi 10,000, ban san me ake iki ba. A haka wani ya turo min da sako na batancin da aka yi. Ina ganin wannan na san cewa saka hoto ya koma wani abu. na daban"

A kan martanin da abokan sana'arta 'yan Kannywood suka yi, Rahama ta ce su ya kamata su fara ankarar da ita.

"Amma babu mamaki wadanda suke martanin sun gani kafin ni amma ba za su iya kira na ba, sun gwanmaci su bari a yi ta cece-kuce akai,” in ji ta

Jarumar ta ce da ace cece-kucen mutane ne kadai ba za ta damu ba. Amma ta ce yin batanci ga Annabi SAW ya sa ta kadu kuma shi ya sa ta ga ya kyautu ta fito ta bayar da hakuri saboda haushin da ta ji na cin mutunci addininta da aka yi.

"Duk wani musulmi dole ya ji haushi, shi ya sa na fito na ba jama'a hakuri kuma na nisanta kai na da kalaman da aka yi."

KU KARANTA KUMA: Tsaro: Matawalle ya saka wa sarakunan gargajiya da wasu shugabanni sabon takunkumi

Jarumar ta ce wannan dalilin ne ya sa ta je ta ciro hoton gaba daya. A cewarta idan da maganganun mutane ne kawai da suke yi game da hotunan ba za ta damu ba.

A gefe guda, kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta Najeriya, MOPPAN ta sake korar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, sakamakon wallafa zafafan hotunan ta a dandalin sada zumunta da hakan ya janyo batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel