Tsaro: Matawalle ya saka wa sarakunan gargajiya da wasu shugabanni sabon takunkumi
- Gwamnan jihar Zamfara ya bada umarni muhimmi ga dukkan sarakunan gargajiya da kuma shugabbanin kananan hukumomi
- Gwamnan ya ce bai amince wani basarake ko wani shugaban karamar hukuma ya sake kwana a wajen masarautarsa ba ko karamar hukumarsa
- Ya sanar da masu assasa rashin tsaro a jihar cewa wannan saukin da suke gani a baya zai kaura inda zai tabbatar ya yi maganinsu
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya umarci dukkan sarakuna da shugabanni na jihar da su mayar da hankalinsu wurin zama a masarautunsu tare da kiyaye zuwa waje suna kwana.
Ya sha alwashin yin maganin dukkan masu bada gudumawa a yankin wurin ta'azzarar rashin tsaro. Ya ce dukkan mai sarautar da aka kama zai rasa kujerarsa.
Gwamna Bello Matawalle ya sanar da hakan ne yayin bude taron kwana daya a kan tsaro wanda yayi da sarakunan gargajiya, malamai da kuma shugabannin cibiyoyin tsaro a jihar.
"Daga yanzu, babu basaraken da ke da damar kwana a wajen masarautarsa. Dole ne ku kasance tare da jama'arku kuma kuna shawo kan matsalolin tsaro a yankunanku", Matawalle ya sanar da su.
"Ga wadanda ke taimaka wa rashin tsaro a jihar nan, ina ce muku ya isa haka. Za mu mayar muku da bakar muguntarku kuma za ku fuskanci fushin da baku taba gani ba," Matawalle ya ja kunnen masu assasa rashin tsaro a jihar.
Ya ce gwamnatin jihar ta kasance mai sauki saboda ganin yadda ake fuskantar matsalar da kuma dukkan kokarin ganin an kawo zaman lafiya a jihar
Kamar yadda Daily Trust ta wallafa, ya ce wannan saukin kan shine wasu 'yan siyasan ke amfani da shi wurin ruruta wutar rashin tsaro a jihar.
"Dukkan shugabannin kananan hukumomi na jihar ana umartar su da su dinga kasancewa tare da jama'arsu saboda sune shugabannin tsaron. A don haka, haramun ne garesu su kwana a wani wuri da ba karamar hukumarsu ba, ba tare da dalili mai kyau ba." Gwamnan yace.
KU KARANTA: EndSARS: Buhari ya aike wa matasa muhimmin sako ta hannun Gambari da sarakuna
KU KARANTA: Za a raba kyautar mita sama da miliyan 1 ta wutar lantarki - Buhari
A wani labari na daban, gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rufe sansanin 'yan gudun hijira a ranar Laraba a jihar, kuma ta umarci mutane 27,000 su koma kauyukansu.
Kwamishinan matasa da habaka wasanni na jihar, Alhaji Sani Danlami, ya bayyana hakan ga manema labarai a gidan gwamnatin jihar, inda yace za a rufe sansanin gudun hijirar da ke Dandume, Faskari, Kankara, Batsari, Jibia, ATC Katsina da gidan marasa gata da ke Katsina.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng