Rahama Sadau ta nemi afuwa bisa sabbin hotuna da ta fitar

Rahama Sadau ta nemi afuwa bisa sabbin hotuna da ta fitar

- Hotunan sun janyo zazzafar muhawarar data tilasta jurumar goge su ba tare da bata lokaci ba

- Wasu na ganin cewa bai kamata jarumar ta wallafa hotana da shiga ta rashin da'a irin wannan ba

- Ta ce ita mai bin koyarwar addinin musulunci ce da kuma Annabi Muhammad (SAW)

Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta bawa masoyanta haƙuri bisa sakin wasu hotuna a shafin ta na Instagram da Tuwita a ranar litinin.

Da yawa daga cikin masoyanta sun ce hotunan basu dace da addinin musulunci da kuma al'adun arewa ba.

Wasu daga cikin masoyan nata kuma basu amince da hakan ba.

Wallafa hotunan ya haddasa zazzafan muharawara tsakanin masoyanta,inda hotunan suka zama ababen maganganu.

Rahama Sadau ta nemi afuwa bisa sabbin hotuna da ta fitar
Rahama Sadau. Hoto @bbchausa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An yi jana'izar jakadar Najeriya a Jordan, Haruna Ungogo a Kano

A hotunan,an gano hoton jarumar sanye da riga mai buɗaɗɗen baya wadda ta ɗame mazaunanta.

Da yawa daga cikin masoyan sun maida zafafan raddi akan hotunan,wanda hakan ya janyo jayayya mai ɗumi a shafunkanta na sadarwa.

Wasu sun ce bai kamata a matsayinta na Musulma ta saki hotunan ta da irin wannan shigar ba.

Masoyanta sun ce bai kamata ta ƙarfafa shigar nuna tsiraici ba.

Muhawarar tayi zafin da ya janyo dole jarumar ta goge sharhi da kuma goge hotonan da ta wallafa daga fejin ta. Sannan ta bada hakuri saboda hotonan da ta saka suka janyo muhawarar.

KU KARANTA: Musulmi sun cigaba da zanga-zanga kan ɓatanci da aka yi ga Manzon Allah

Ta ce: "abin bakin ciki ne wanda banyi zato ba na tashi na tarar da sakonnin da banyi tsammani ba, saboda hotonan dana wallafa marasa cutarwa. A matsayin Mutum, wasu sun bani dariya, wasu sun bani haushi wasu kuma ban amince dasu ba. Babban abin bacin ran shine wasu sun dauki wata ma'anar daban.

"Cikin girmamawa, ina nisanta kaina daga irin munanan da kuma kalaman batancin. Ga duk wanda ya sanni kuma yake bibiyata, yasan cewa ni ba mai kula duk wani abu ku karbar shawara daga wajen yan bakan shafukan sadarwa. Sai daga annabi na da kuma addini na dana samu tarbiya.

A wani labarin, Aƙalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya faru a yammacin ranar Asabar a kasuwar Akungba ta Jihar Ondo.

An ruwaito cewa hatsarin ya faru ne a lokacin da wata trela da ƙwace wa direban ta kutsa cikin kasuwar Akungba ta take mutum 10 har lahira tare da raunata wasu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164