Faduwar Trump zai kawowa Najeriya da wasu kasashe cinikin $700bn, cewar Masana

Faduwar Trump zai kawowa Najeriya da wasu kasashe cinikin $700bn, cewar Masana

- Nasara Joe Biden kan Trump zai janyowa Najeriya alheri na hannun jari

- Masana tattalin arziki sun bayyana akwai attajiran da suka shirya shiga kasashe masu tasowa Trump na fadi

- Trump ya shiga takun saka ta kasuwanci na kasar Sin kuma hakan na shafan sauran kasashen duniya

Nasarar tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka, Joe Biden, a zaben da aka kusa kammalawa zai janyo hannun jarin $7000bn ga Najeriya da wasu kasashe masu tasowa, masanan Renaissance Capital (RenCap) sun yi hasashe.

Shugaban masanan tattalin arzikin RenCap, Charles Robertson, ya ce nasarar Biden zai kawo tiriliyoyin dala Najeriya.

A rahoton da masanan suka yiwa masu sanya hannun jari mai take: "Nasarar Biden, Tiriliyoyi da zasu shiga kasashe masu tasowa da kulle" kuma aka saki ranar Alhamis, Robertson ya yi bayanin cewa idan hakan ya faru, mutane zasu fahimci dalilin da yasa yan takara ke gwara kan juna a zaben.

DUBA NAN: Kudi N1.3bn ya yiwa asibitin fadar shugaban kasa kadan - Sakataren Aso Villa

Masanan cibiyar binciken sun ce suna kyautata zaton cewa da yammacin yau idan sakamakon jihar Nevada ta fito, Biden zai lashe.

A kan hasashen da ake yiwa Najeriya da wasu kasashe masu tasowa, Robertson ya ce fadin Donald Trump a zaben nan abu ne mai kyau ga kasuwanninmu.

Ya ce masu sa hannun jari a fadin duniya zasu fara dawo da kudadensu kasuwanni masu tasowa sosai.

Ya alanta cewa tun yanzu, shugaban sashen ajiyan kudin kamfanin Blackrock, wanda ke da alhakin dukiyoyin kamfanin na $2.6 trillion kuma ya yi alkawarin zasu zuba kudin cikin kasuwanni masu tasowa.

Faduwar Trump zai janyowa Najeriya da wasu kasashe cinikin $700bn, cewar Masana
Faduwar Trump zai janyowa Najeriya da wasu kasashe cinikin $700bn, cewar Masana
Asali: UGC

KU KARANTA: Jerin lokutan da Buhari ya tafi jinya Ingila tsakanin 2015 da yanzu

Mun kawo muku cewa Jihohi biyu da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ke sa ran ci domin samun nasara a zabe sun fara kubucewa daga hannunsa.

A jihar Pennsylvania, ranar Laraba bayan zabe Trump ya zarcewa Biden da kuri'a sama da 500,000, amma a yanzu haka, tazarar ta sauko dubu 22,389 kuma saura kuri'u sama da 100,000 da ba'a kirga ba tukun daga birnin Philadelphia kuma yawancin masoyan jam'iyyar Democrat ne.

Ga yadda sakamakon yake yanzu haka a Pennsylvania:

Trump - 3,285,239

Biden - 3,262,850

A jihar Georgia kuwa, Dan takaran shugaban kasar Amurka karkashin jagorancin Joe Biden ya zarcewa Donald Trump a jihar Georgia da kuri'u 917, kuma haar yanzu ba'a kammala kirga ba.

Idan Biden ya samu nasara a Georgia, zai zama dan jam'iyyar Democrat daya da ya ci zaben jihar tun 1992.

Ga yadda sakamakon zaben gaba daya yake:

Biden - 73,534,059 | 50.46%

Trump - 69,799,702 | 47.9%

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel