Kudi N1.3bn ya yiwa asibitin fadar shugaban kasa kadan - Sakataren Aso Villa
- Sanatoci sun bukaci ma'aikatan asibiti fadar shugaban kasa su daina bari Buhari na fita kasar waje jinya
- Sanata Danjuma Laah ya ce bai kamata a rika yawo da shugaban kasa idan yana rashin lafiya ba
- Sakataren fadar shugaban kasan ya ce yana bukatan kudi fiye da wanda ake shirin bashi
Sakataren din-din-din fadar shugaban kasa, Tjjani Umar, ya ce kudi bilyan 1.3 da aka tanadarwa asibitin fadar shugaban kasa a kasafin 2021 ya yi kadan.
Ya bayyana hakan a hirarsa da manema labarai ranar Alhamis bayan kare kasafin kudin 2021 da ma'aikatarsa ta gabatar gaban kwamitin harkokin gwamnati, Punch ta ruwaito.
Umar wanda yayi alkawarin tabbatar da cewa shugaban kasa, iyalansa da manyan jami'an gwamnati sun samu isasshen kayan lura da lafiya idan aka amince da kudin.
"Kudi N1.3bn gaskiya ya yi kadan idan ka hada da kudin da muka bukata, kudi, " yace.
"Idan aka kwatanta da asibitocin duniya, za ku ga cewa wannan kudi bai yi kusa ko kadan da abinda muke bukata ba."
"Mun dauki wannan asibitin aiki mai muhimmanci saboda muna son kafa tarihi ".
KAI TSAYE: Sakamakon zaben kasar Amurka sun fara fitowa, Trump 214, Biden 264
KU KARANTA: Jerin lokutan da Buhari ya tafi jinya Ingila tsakanin 2015 da yanzu
A ranar Alhamis ne majalisar dattijai ta gargadi ma'aikatan fadar shugaban kasa (Asorock Villa) su dakatar da shugaba Buhari daga fita waje domin a duba lafiyarsa.
A cewar majalisar, yin hakan zai tabbatar da cewa asibitin fadar shugaban kasa ya koma hayyacinsa a cikin shekarar nan.
Kwamitin majalisar dattijai a kan tabbatar da daidaito da alaka a tsakanin bangarorin gwamnati ne ya yi wannan gargadi yayin da babban sakataren fadar shugaban kasa, Tijjani Umar, ya bayyana a gabansa domin kare kasafi kudin shekarar 2021.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng