Bullar sabuwar cutar alakakai ta hallaka matasa fiye da 30 a Nigeria

Bullar sabuwar cutar alakakai ta hallaka matasa fiye da 30 a Nigeria

- A yayin da ake sallama da cutar korona, wata sabuwar cuta ta bulla a karamar hukumar Ika North East a jihar Delta

- Cutar ta alakakai ta yi sanadin mutuwar matasa ƴan shekaru tsakanin 18 zuwa 25 a wasu garuruwa guda biyu

- Wadanda cutar ta kashe su kanyi zazzabi mai zafi da aman jini, ciwon kai, da ciwon jiki

Adadin yawan mace-mace sakamakon wata cuta mai sarƙaƙiya da ta addabi yankin al'ummomin Ute Okpu, Ute Erumu, da Idumusa a ƙaramar hukumar Ika North East dake Jihar Delta ta ci rayuka fiye 30.

A ƙarshen makon nan ne gwamnatin jihar Delta ta farga da mutuwar matasa ƴan shekaru tsakanin 18 zuwa 25 a wasu garuruwa guda biyu.

Ana zargin matasan na rasa rayukansu ne sakamakon zazzaɓin borin jini ko gurɓacewar sinadarai.

DUBA WANNAN: Taron gwamnoni da sarakunan arewa abin kunya ne ga yankin - CNG ta yi caccaka

Bincike ya tabbatar da cewa wasu daga cikin mamatan suna aman jini kafin mutuwarsu, wasu suna ƙorafin ciwon jiki, ciwon kai da zazzaɓi kafin su cika a gida ko asibiti.

Mrs Monica Emeke ta rasa ƴa'ƴanta biyu a sanadiyyar sabuwar cutar, ɗanta mai shekaru 26, da yarta budurwa, mai shekaru 21, duk sun rasu sakamakon cutar.

Bullar sabuwar cutar alakakai ta hallaka matasa fiye da 30 a Nigeria
Cibiyar killace masu cutar korona a jihar Delta
Asali: Facebook

Ta bayyana cewa sabuwar cutar ta kashe mutum biyar a garin Ute Okpu a rana ɗaya kacal.

An samu rahotannin mace-mace daga maƙwabtan ƙauyuka da suka haɗa da Ute Erumu.

DUBA WANNAN: Ku dakatar da Buhari daga fita waje domin duba lafiya - Majalisa ta gargadi fadar shugaban kasa

Gwamnatin jihar ta tabbatarwa da mazauna yankin da abin ya shafa tana iyakacin bakin ƙoƙarinta don kawo ƙarshen cutar.

Kwamishinan lafiya Dr Mordi Ononye, shine ya tabbatarwa mazauna yankin cewa za'a kawo ƙarshen cutar lokacin da suka kai ziyara da tawagarsa ta jami'an lafiya don nazarin cutar.

A ranar Laraba ne Legit.ng ta rawaito cewa gwamnatin tarayya na shirin rancen ƙuɗi kimanin Dala biliyan 1.2 daga ƙasar Braziƙ don bunƙasa harkar noma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel