Taron gwamnoni da sarakunan arewa abin kunya ne ga yankin - CNG ta yi caccaka

Taron gwamnoni da sarakunan arewa abin kunya ne ga yankin - CNG ta yi caccaka

- Gwamnoni, sarakuna, da sauran wasu manya daga arewa sun gudanar da wani muhimmin taro a Kaduna

- An gudanar da taron ne domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi kasa musamman yankin arewa

- Sai dai, gamayyar kungiyoyin arewa (CNG) ta bayyana taron a matsayin abin kunya da kaucewa hanya

Haɗakar ƙungiyoyin Arewa (CNG) ta bayyana taron da ya wakana baya-baya nan tsakanin ƙungiyar gwamnonin Arewa (NGF) da Sarakunan gargajiya a matsayin abin kunya.

Ƙungiyar tace taron abin kunya ne tunda sun gaza tattauna batutuwan da suka addabi yankin arewa da ƴan-arewa,musamman matsalar tsaro da zamo ƙarfen ƙafa a yankin.

Mai magana da yawun ƙungiyar CNG, Abdul'azeez Suleiman, ne ya faɗi hakan yayin taro da manema labarai, inda ya bayyana cewa an bauɗe hanya gava ɗaya daga inda ƙudirin taron ya dosa.

KARANTA: Magidanci ya yi garkuwa da diyarsa a Kano, ya bukaci matarsa ta biya N2m kudin fansa

"Taron ya fi karkata da bada muhimmanci ga zanga-zangar #EndSARS da abubuwan dake faruwa a kafafen sadarwar zamani, wanda kwata-kwata babu su a ajandar shirya taron.

"Maimakon tattauna batutuwan da suka shafi arewa a lokacin sun ɓuge da wasu batutuwan na daban.

"Ƙungiyar Arewa da kuma akasarin al-ummar arewa sun ji kunya ace taron gwamnoni da sarakunan arewa da wakilan da muka zaɓa da kuma masu manyan muƙaman tarayya daga arewa sun fi jin daɗin tattauna wasu abubuwa can daban kamar zangar-zangar#EndSARS da makamantan su, mu kuma sunyi burus da matsalolinmu masu matuƙar muhimmanci da suka addabe mu, musamman rashin tsaro.

Taron gwamnoni da sarakunan arewa abin kunya ne ga yankin - CNG ta yi caccaka
Taron gwamnoni da sarakunan arewa abin kunya ne ga yankin - CNG ta yi caccaka
Asali: UGC

"Basu dubi dukkan matsalolinmu da suka haɗar da; lalacewar matasa, rashin aikin yi, ɓaƙin talauci, taɓarɓarewar harkar noma, da kuma karyewar tattalin arziƙin yankin bakiɗaya ba.

KARANTA: Magidanci ya gutsure ƴan-yatsun matarsa uku ta hanyar gantsara mata cizo

"Ba mu ji daɗin yadda taron ya wakana ba, abin kunya ne, tirr da Allahwadai, ace an kasa samun zaƙaƙurin da zai yi magana akan matsayar arewa sabanin ƙirƙirarrun labaran ƙanzon kurege akan kaiwa masu zanga-zanga a Lekki hari wanda suka ce ya na neman janyo damuwa a ƙasashen duniya.

"Bamu ji daɗin yadda taron ya gaza tattauna yadda za'a tallafawa ƴan arewa da kaiwa farmaki, aka lalata dukiyoyinsu, aka kashe wasunsu da basu ji ba, basu gani ba, babu gaira babu dalili."a cewarsa.

Ya kara da cewa tuni sun yi nisa wajen tattara alƙaluman ƴan arewa da aka raba da muhallinsu, aka kashe a kudancin ƙasar nan.

A wani labarin Legit.ng da ta wallafa, Sojojin Amurka na tawagar SEAL Team Six sun yi nasarar kubutar da Philip Walton, ɗan ƙasar Amurka mai shekaru 27, wanda akayi garkuwa dashi aka boye Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel