DPO ya gurfanar da tela a gaban kotu saboda ya yi masa dinkin banza

DPO ya gurfanar da tela a gaban kotu saboda ya yi masa dinkin banza

- Harkar kasuwanci tsakanin DPO da tela ta kare a gaban kuliya manta sabo

- DPO ya gurfanar da telansa a gaban kotu bisa tuhumarsa da saba yarjejeniyar da suka yi kafin ya bashi dinki

- Lauyan da ke kare telan a kotu ya ce DPO ne alkalin shari'ar, shi ne mai gurfanarwa da kuma gudanar da bincike

DPO mai kula da ofishin rundunar ƴansanda da ke Iyaganku a Ibadan ta jihar Oyo, Alex Gwazarzah, ya gurfanar da mai ɗinkinsa, Lukman Adeniyi, a gaban kotu sakamakon baiwa ɗan koyo kayansa ya ɗinka.

Tirka-tirkar ta fara lokacin da DPO ya zargi telan cewa ya ɓata masa kayansa.

KARANTA: Magidanci ya yi garkuwa da diyarsa a Kano, ya bukaci matarsa ta biya N2m kudin fansa

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴansanda, Olugbenga Fadeyi, ya bayyana cewa; "DPO Gwazarzah yayi yarjejeniya da telan nasa akan shi zai ɗinka kayan da kansa, amma sai telan ya saɓa alƙawari ya bawa wani can daban."

"Kwamishinan ƴansandan ya shiga maganar don shawo kan lamarin."

Telan ya ce wani tsohon abokin cinikayyarsa da suka shafe sama da shekaru goma ne ya gabatar dashi gun DPO Gwazarzah.

DPO ya gurfanar da tela a gaban kotu saboda ya yi masa dinkin banza
DPO ya gurfanar da tela a gaban kotu saboda ya yi masa dinkin banza @Thenation
Asali: Twitter

Adeniyi ya ce wai dama DPO din ya ci mutucina bisa zargin bai ɗinka masa kayan da kyau ba.

"Bayan DPO ya wanka min mari, ya sa hannu ya karɓe kayansa guda 12 ba tare da biyan kuɗin aikina ₦60,000 da mukayi yarjejeniya ba.

"Ranar 1 ga watan Nuwamba ya ce nazo na karɓi kuɗina, kawai sai ya garƙame ni a ofishin su", a cewar telan.

KARANTA: Kano: Mijina ya na tilasta min akan lallai sai na bashi damar shan jinin al'adata - Matar aure a gaban kotu

Rahotanni sun ce an bada belin telan a ranar Litinin 2 ga watan Nuwamba, an kuma shigar da ƙara ranar Talata, 3 ga wata..

An gurfanar da Adeniyi a kotu mai lamba takwas 8, kotun Majistire, da ke Iyaganku kamar yadda kundin ƙarrarraki mai lamba MI/881C/2020 ya nuna.

DPO yana tuhumar wanda ya kai ƙarar da lalata masa kayansa na kimanin ₦181,000 da ya bashi dinki tun watan Satumba.

Gwazarzah yace bai gamsu da aikin da telan yayi masa ba.

Yayi kafe akan cewa telan ya saɓawa yarjejeniyarsu ta hanyar bawa yaron shagonsa kayan ya ɗinka.

Mai shari'a, Olajumoke Akande, ta bada belin wanda aka yi ƙarar akan kuɗi ₦50,000 tare da mutane biyu masu tsaya masa.

Ta kuma ɗage cigaba da sauraron ƙarar zuwa 17 ga watan Nuwamba.

Lauyan wanda ake zargin , Jubril Olanrewaju, yace "DPO shine alƙalin shari'arsa. Shi ne wanda ya yi bincike, kuma ya tilastawa telan rubuta jawabai a ofishinsu na Iyaganku. Kuma har wa yau dai shi ne wanda yasa hannu a takardar tuhuma."

A wata shari'ar da Legit.ng Hausa wallafa labarinta, hukumar ICPC ta bankado badakalar da wani rijistaran babban kotun tarayya da ke Kaduna ya tafka da kudin kotu N80m.

A ranar Alhamis ne Legit.ng Hausa ta wallafa cewa majalisar dattijai ta gargadi ma'aikatan fadar shugaban kasa (Asorock Villa) ta dakatar da shugaba Buhari daga fita waje domin a duba lafiyarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel