Kuliya manta sabo: Alkali ya daure rijistaran kotun Kaduna a kan gararumar N80m

Kuliya manta sabo: Alkali ya daure rijistaran kotun Kaduna a kan gararumar N80m

- Rijistaran kotu ya yi amfani da kudin da mai laifi ya ajiye wajen sayen manyan kadarori a manyan biranen Najeriya

- Hukumar ICPC ta bankado badakalar da rijistaran mai suna Mista Joseph Udo ya tafka

- Bayan ICPC ta kwace kadarorin da ta gano daga hannun Mista Udoh, ta gurfanar da shi a gaban kotu

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Kaduna ta zartar da hukuncin daurin shekaru hudu a kan tsohon rijistaran kotun, Mista Joseph Etefia Udoh, bayan ya amsa laifin almundahana da kudin kotu N80m.

Hukumar ICPC ce fara gurfanar da Mista Udoh da matarsa, ma'aikaciyar babbar kotun tarayya da ke Abuja, a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja tun cikin watan Disamba na shekarar 2019 bisa tuhuma guda goma sha biyu.

Ana tuhumar Mista Udoh da matarsa mai suna Grace Udoh da gararumar kudi N80m da wani mutum da ake kara ya ajiye a kotun.

DUBA WANNAN: Magidanci ya yi garkuwa da diyarsa a Kano, ya bukaci matarsa ta biya N2m kudin fansa

Mista Udoh ya zuba kudin a asusun matarsa tare da yin amfani da su wajen sayen manyan kadarori a manyan biranen Najeriya.

Kuliya manta sabo: Alkali ya daure rijistaran kotun Kaduna a kan gararumar N80m
Mista Joseph Udoh @daily_nigerian
Asali: Twitter

Bayan Mista Udoh ya nemi sulhu, an rage yawan tuhumar da ake yi masa zuwa guda hudu yayin da aka ajiye dukkan tuhumar da ake yi wa matarsa.

Bayan an karanta masa dukkan tuhumar da ake yi masa, Mista Udoh ya amince tare da amsa dukkan laifukansa.

DUBA WANNAN: Magidanci ya gutsure ƴan-yatsun matarsa uku ta hanyar gantsara mata cizo

Lauya mai gabatar da kara, Shehu Yahaya, ya roki kotun ta yankewa Mista Udoh hukunci bisa tanadin da doka ta samar na amincewa da sulhu kamar yadda ya ke a karkashin sashe na 270(10) na kundin hukuncin manyan laifuka na shekarar 2015.

Da ya ke karanta hukuncin da kotu ta yanke, Jastis P. H. Mallong ya aika Mista Udoh zuwa gidan yari na tsawon shekara guda.

Kazalika, kotun ta yanke hukuncin cewa ICPC za ta rike dukkan kadarorin da ta kwace daga hannun Mista Udo tare da yin gwanjonsu.

A ranar Alhamis ne Legit.ng Hausa ta wallafa cewa majalisar dattijai ta gargadi ma'aikatan fadar shugaban kasa (Asorock Villa) ta dakatar da shugaba Buhari daga fita waje domin a duba lafiyarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel