Mijina ya na tilasta min akan lallai sai na bashi damar shan jinin al'adarta - Matar aure a gaban kotu

Mijina ya na tilasta min akan lallai sai na bashi damar shan jinin al'adarta - Matar aure a gaban kotu

- Abun ya daurewa jama'a kai bayan wata matar a Kano ta sanar da kotu cewa mijinta ya na tilasta mata a kan sai ya dinga shanye jinin al'adarta

- Matar ta yi zargin cewa mijin nata ya na son ya ke shan jinin al'adar ne saboda dalilan tsafi

- A cewar matar, mijinta ya koyi siddabaru a saboda haka ta roki kotu ta datse igiyar aurensu

Wata mata a jihar Kano ta gurfanar da mijinta a gaban alƙali tana roƙon a datse igiyar aurensu da shi.

Matar ta shigar da ƙarar ne a gaban kotun shari'ar musulunci mai lamba ta ɗaya da ke ƙarƙashin alƙali Abdullahi Halliru Ƙofar Na'isa.

Matar ta yi iƙirarin cewa mijinta ya yi mata siddabaru tare da tilasta mata akan lallai sai ta bashi damar shan jinin al'adarta don cimma buƙatunsa.

Shi kuma mijin nata ya turje tare da ƙaryata iƙirarin matar tasa, inda ya ce zuƙi ta malle kawai ta yi masa.

DUBA WANNAN: Zaben shugaban kasar Amurka: An saka dokar ta baci a jihar Oregon

Sai dai, kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa huɗu ga watan Disamba, 2020 domin tattara hujjoji da shaidu.

Lauyan wadda ta shigar da ƙara Barista Abdulrashid Balarabe Adam Ɗandago ya yi ƙarin haske kan iƙirarin matar a zaman kotun da aka yi ranarb Litinin.

Mijina ya na tilasta min akan lallai sai na bashi damar shan jinin al'adarta - Matar aure a gaban kotu
Zaman kotu
Asali: Facebook

Sai dai, gogan mijin matar ya ce zai bayar da al-ajabi a ranar da za'a sake zaman sauraron ƙarar.

A wani labari mai kamanceceniya da wannan, Legit.ng Hausa ta rawaito cewa Funke Adejomo, marubuciyar Najeriya kuma fasto a cocin Agape Ministries, ta bayyana cewa duk macen da arziƙin mijinta ya karye bayan ya aureta, bata da maraba da mayya.

DUBA WANNAN: Kotu ta datse igiyar auren shekara 10 bayan mata ta zargi miji da halin bera

Ta faɗi hakan lokacin da take magana akan irin muhimmiyar rawa da yakamata mata su taka a gidan mazajen su yayin wa'azi a coci.

Lokacin da take yin huɗuba, Funke ta caccaki mata masu bajewa a gidan miji suyi ta haifar ƴa'ƴa kuma su bar mazajensu da wahala.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: