Yanzu Yanzu: Gobara ta kama ma’adanar tankokin mai na OVH

Yanzu Yanzu: Gobara ta kama ma’adanar tankokin mai na OVH

- Gobara ta kama ma’ajiyar tankokin mai na OVH a unguwar Apapa, jihar Lagas

- Ba a san abun da ya haddasa gobarar ba wacce ke ci gaba da ci har yanzu

- Hukumar kashe gobara ta jihar da hadin guiwar sauran hukumomi na kokarin shawo wutar dake ci gaba da ci a yanzu haka

Labari da ke zuwa mana ya nuna cewa ma’ajiyar tankokin mai na OVH da ke yankin Apapa a jihar Lagas na nan tana ci da wuta a yanzu haka.

Ba a san ainahin abunda ya haddasa gobarar ba wacce ta fara ci a safiyar yau Alhamis, 5 ga watan Nuwamba ba.

Sai dai kuma masu aikin ceto na ta kokarin kwashe mutanen da ke cikin harabar wajen a lokacin da gobarar ta fara, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Bashin $1.2bn: Kar ka mayar da Nigeria ƙasar mabarata - PDP ta gargaɗi Buhari

Yanzu Yanzu: Gobara ta kama ma’adanar tankokin mai na OVH
Yanzu Yanzu: Gobara ta kama ma’adanar tankokin mai na OVH Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) na reshen, Ibrahim Farinloye, wanda ya tabbatar da afkuwar al’amarin ya ce an yi nasarar kwashe dukkanin ma’aikatan wajen.

Ya ce an tura yan kwana-kwana daga hukumar kula da jiragen ruwa ta kasa (NPA), hukumar kashe gobara ta tarayya da kuma hukumar kula da tsaron Teku ta kasa (NIMASA) zuwa wajen da abun ya faru domin su kashe gobarar.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun saki alkalan Zamfara da suka yi garkuwa da su bayan an biya kudin fansa

A wani labarin, Kamfanin man feturin Najeriya NNPC ya tabbatar da aukuwar gobara a ma'ajiyar hakar manOML 40 dake kamfanin cigaban man feturin Najeriya NPDC ke amfani.

A jawabin da dirakta manaja na sashen hulda da jama'a na hukumar, Kennie Obateru, ya saki, ya ce gobarar ta faru ne yayinda ake sarrafa mai a Gbetiokun, The Cable ta ruwaito.

Kamfanin ya ce babu wanda ya mutu kuma babu wanda ya samu rauni. Hakazalika fashewar bai haifar da wani watsuwar mai cikin ruwa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel