Yanzu-yanzu: Gobara ta kama ma'ajiyar hakar mai ta NNPC, OML 40

Yanzu-yanzu: Gobara ta kama ma'ajiyar hakar mai ta NNPC, OML 40

- Kamfanin NNPC ya saki jawabi kan gobarar da ta ci OML 40 ranar Talata

- Ba'ayi rashin rai da samun rauni ba amma an yi asarar dukiya

- Najeriya zata fuskanci matsalar hakar mai sakamakon wannan gobarar

Kamfanin man feturin Najeriya NNPC ya tabbatar da aukuwar gobara a ma'ajiyar hakar manOML 40 dake kamfanin cigaban man feturin Najeriya NPDC ke amfani.

A jawabin da dirakta manaja na sashen hulda da jama'a na hukumar, Kennie Obateru, ya saki ranar Talata, ya ce gobarar ta faru ne yayinda ake sarrafa mai a Gbetiokun, The Cable ta ruwaito.

Kamfanin ya ce babu wanda ya mutu kuma babu wanda ya samu rauni.

Hakazalika fashewar bai haifar da wani watsuwar mai cikin ruwa ba.

"Amma wutar ta yiwa gangan ajiyar mai MT Harcourt mumunar barna, wacce ke taimakawa wajen hakan gangan mai 10,000 kulli yaumin, " jawabin yace.

NNPC ya kara da cewa an kaddamar da bincike domin sanin abinda ya haddasa gobarar domin kiyaye gaba.

KU KARANTA: 'Yan shi'a sun ƙona tutar Faransa a Abuja kan kalaman shugaban Faransa, Macron

Yanzu-yanzu: Gobara ta kama ma'ajiyar hakar mai ba NNPC, OML 40
Yanzu-yanzu: Gobara ta kama ma'ajiyar hakar mai ba NNPC, OML 40 Hoto: NNPC
Asali: Twitter

A wani labarin daban, fusatattun matasa a garin Daudu a ƙaramar hukumar Gina, a ranar Talata, sun ƙona Divine Shadow Church kan alaƙanta mai cocin da satar mazakuta a garin kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kwana ki uku da suka shuɗe, matasan sun yi zanga zanga a babban titin Makurdi - Lafia kan abinda suka kira 'batar mazakutar' mutum shida cikin wata guda a garin.

KU KARANTA: Buhari ya zagaye kansa da 'yan iska masu sharara masa karya - Father Mbaka

Matasan da suka ƙona cocin sun yi ikirarin cewa mai cocin, Manzo Uhembe da wani da suka haɗa baki, Noah Saka ne masu kitsa yadda ake satar mazakutar.

Nongu Francis, wani da ya yi iƙirarin cewa wani mutum daban da ya kashe kansa ya sace masa mazakuta a ranar 10 ga watan Oktoba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng