Magidanci ya gutsure ƴan-yatsun matarsa uku ta hanyar gantsara mata cizo

Magidanci ya gutsure ƴan-yatsun matarsa uku ta hanyar gantsara mata cizo

- Wani magidanci ya saka kaifin fikar hakoransa ya gartsawa matarsa cizo har ta kai ga ya guntule mata yatsu uku

- Magidancin ya amsa laifinsa a gaban kotu tare da neman sassauci a hukuncin da Alkali zai zartar

- Sai dai, Alkalin kotun ya umarci rundunar 'yan sanda ta cigaba da tsare agidancin har zuwa lokacin da matarsa da ke jinya a asibiti za ta warke

Wata kotun Majistire a Abuja a ranar Laraba ta bawa rundunar 'yan sanda umarnin su cigaba da tsare wani bakanike mai shekaru 45, Amusu Olajide, wanda ya amsa laifin gantsarawa matarsa cizo har ta kai jallin ya guntule mata ƴan-yatsu uku a hannunta.

Bayan ya amsa laifinsa, magidancin ya roƙi sassauci a hukuncin da alƙali zai zartar.

Ƴan sanda sun tuhumi Olajide, wanda yake zaune a ƙauyen Gui da yankin Sunka a Abuja, da laifuka nau'i biyu.

KARANTA: Kotu ta datse igiyar auren shekara 10 bayan mata ta zargi miji da halin bera

Laifi na farko shine mummunan yunƙurin kisa da kuma na biyu azabtarwa mai tsanani.

Mai shari'a Yusuf Ibrahim ya bada umarnin ƴan sanda su cigaba da tsare mai laifin har sai an sallami majinyaciyar matarsa daga asibiti.

Magidanci ya gutsure ƴan-yatsun matarsa uku ta hanyar gantsara mata cizo
Magidanci ya gutsure ƴan-yatsun matarsa uku ta hanyar gantsara mata cizo
Asali: Getty Images

Alƙali ya ɗage cigaba da sauraron ƙarar zuwa 18 ga watan Nuwamba don zartar da hukunci.

Lauya mai gabatar da ƙara Abdullahi Tanko, ya gayawa kotu cewa yansanda sun sami bayanan yadda wanda ake zargin ya kulle matarsa wadda suke da ƴa'ƴa huɗu tare a ranar 20 ga watan Oktoba bayan sun yi faɗa.

KARANTA: Ke mayya ce idan mijinki ya tsiyace bayan kun yi aure - Malamar Mata

Tanko ya sanar da kotun cewa mijin ya sha yin ikirari da yunƙurin cakawa matarsa mai suna Bose wuka.

Daga bisani ne kuma ya sa kaifin haƙoransa ya guntulewa matar tasa yatsunta uku.

Tanko ya ce da kyar Mr Enoch Barnabas, mai gidan hayar da ma'auratan ke zaune, ne ya ceci matar.

Laifin ya saɓawa kundin shari'a na 265 da 241.

A wani labarin mai alaka d wannan da Legit.ng ta wallafa, kotu ta datse igiyar auren shekara 10 bayan mata ta zargi miji da halin bera.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel