Da duminsa: Gwamnatin Kaduna ta dage dokar ta-baci a dukkan jihar
- Gwamnatin jihar Kaduna ta dage kullen awanni 24 da ta saka a kananan hukumominta 23
- Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya sanar da hakan a wata takarda
- Ya ce wajibi ne mazauna jihar su kiyaye duk wani abu da zai kawo rikici da tashin hankali
Gwamnatin jihar Kaduna ta dage kullen da ta saka a kananun hukumomi 23 da ke jihar, zuwa karfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma, jaridar The Nation ta wallafa.
A wata takarda da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya saki, ya ce za a dage kullen take-yanke.
Kamar yadda Aruwan yace, "an sanar da shugaban harkokin tsaro wannan labarin, kuma za su cigaba da tsare jihar yadda ya kamata.
"Muna masu sanar da ku cewa gwamnatin jihar Kaduna da jami'an tsaro ba za su dauki duk wani abu wanda zai yi sanadin karya doka ba, komai kankantar shi."
"Ana shawartar mazauna jihar da su cigaba da kula da dokoki, sannan su tabbatar sun sanar da duk wani lamari da suka zargi zai iya kawo barkewar rikici a jihar. Sannan zasu iya sanar da jami'an tsaro idan wata matsala ta taso ta wadannan layukan: 09034000060, 08170189999," a cewarsa.
KU KARANTA: Hotuna: Shekau ya saki sabon bidiyo tare da kananan yara da ya horar, ya aike sako
KU KARANTA: Malami: 'Yan daba sanye da kayan sojoji ne suka yi harbe-harbe a Lekki
A wani labari na daban, 'yan fashi da makamai sun tare hanyar Bakori zuwa Kabomo a jihar Katsina, jaridar Katisna Post ta wallafa hakan.
A ranar Talata da misalin karfe 8:30 na dare ne 'yan fashin suka tare hanyar Bakori zuwa Kabomo. DPO din Bakori ya jagoranci 'yan sanda zuwa wurin, inda suka yi musayar wuta da 'yan fashin, wanda sakamakon haka, daya daga cikin 'yan fashin ya yada bindigar tokarsa, wacce 'yan sandan suka dauke.
An cigaba da bincike don damko wadannan shu'uman mutanen, a cewar kakakin rundunar 'yan sandan, SP Gambo Isah.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng